Kwana biyu bayan tashin na farko, An sako gano wani bam da aka dana a Kaduna.
‘Yansanda a jihar Kaduna sun sake gano wani bam na biyu da aka sake danawa a otal a jihar.
‘Yansandan sun ce sun gano bam dinne a yankin Romi dake karamar hukumar Chukun ta jihar.
Hakan na zuwane awanni 48 bayan da bam na farko ya tashi ranar Lahadin da ta gabata a Kabala.
Kakakin ‘yansandan jihar, ASP Muhammed Jalige ne ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar ga manema labarai ranar Talata.