Kurkuku Yadda na yi rayuwa cikin ‘jahannamar duniya’ a Najeriya.
Alkaluma na Majalisar Dinkin Duniya sun nuna cewa akwai fursunoni fiye da miliyan 11 a gidajen yari a fadin duniya. Fiye da miliyan uku daga cikinsu ana tsare da su ne ba tare da an yi masu shari’a a kotu ba, bare a yi batun hukunci.
Najeriya na daya daga cikin kasashen da lamarin ya fi muni. Akwai fursunoni kusan 70,000 a gidajen yarin kasar, kimanin 75% na zaman jiran shari’a ne a cewar hukumomi, yayin da cunkoso ya yi yawa matuka.
Wasu fursunonin kan kwashe shekara da shekaru ba su san matsayinsu ba, wasu ma kan shafe shekarun da suka zarta tanadin da doka ta yi na hukunci mafi tsanani na laifin da ake zarginsu da aikatawa. Wasu daurarrun kan ma rasa rayukansu.
”Jahannamar duniya”
Yaron mota, Patrick Moses, ya samu ‘yanci, ya komo kan titi a Fatakwal babban birnin Jihar Ribas, bayan kwashe fiye da shekara shida a gidan yari yana zaman jiran shari’a. ‘Yanci ne da ya dade yana fatan samu.
Ya ce ”lokacin da na fito sai na ji kamar wannan wata sabuwar duniya ce.” ‘Yan sanda ne suka kama shi lokacin da suka samu kananan bindigogi biyu nau’in fistil a cikin wata mota safa, yana matsayin yaron motar.
Ya shaida wa BBC cewa ainihin fasinjoji mamallaka makaman sun tsere. Masu fafutikar kare hakkin bil-Adama ne suka taimaka aka sako shi daga jarun. To amma ya bayyana cewa ya ga ukuba a gidan yari.
Patrick ya ce muna kiran gidan yari ”jahannamar duniya” saboda irin wahala da ake sha, da kuma munanan abubuwa da ke faruwa a ciki, yana mai cewa a takaice ”gidan yari babu dadi.”
Matashin mai shekara 31, ya ce kusan a kullum mutane na mutuwa a gidan yarin. Ya kara da cewa kuma idan fursuna ya mutu, gandurobobin ba za su bude kofar kurkukun don fitar da gawar ba, ko da da tsakar dare ne. ”Sai dai ku kwana da gawar, sai gari ya waye” kafin ma’aikatan gidan yarin su zo su fitar da ita.
- Nigeria: Fursunoni 430 sun samu shiga jami’a
- IPOB: Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta zargi ‘yan ƙungiyar da kai hari kan jami’anta a Jihar Imo
- Tsofaffin gwamnonin Najeriya da aka tura gidan yari
Cunkoso babbar matsala ce
Hukumomi sun ce, akwai fursunoni kusan 70,000 a gidajen yarin Najeriya – Kimanin 75% zaman jiran sharia suke yi, saboda rashin nagarta da kuma matukar jinkiri a tsarin shari’a da hukunta laifuka.
A cikin watan Disamba, ministan lamuran cikin gida na Najeriya, Rauf Aregbesola, wanda ma’ikatarsa ce ke kula da gidajen yari a kasar, ya yi nuni da cewa matukar cunkoso da kuma yawan fursunoni da ke zaman jiran shari’a a kasar na daga cikin matsaloli da ke haddasa kai hare-hare a gidajen yari. A cewar shi, ”jinkirta adalci, rashin adalci ne.”
‘Yan bindiga sun fasa gidajen yari da dama cikin kimanin shekara guda da ta gabata, bisa dukkan alamu da nufin kubutar da takwarorinsu da ke tsare. Fursunoni fiye da dubu 5,000 suka tsere, mafiya yawansu ba a kai ga sake kamo su ba, in ji hukumomin kasar.
Jami’ai a Najeriya dai sun amsa cewa tabbas akwai cunkoso a gidajen yarin kasar galibinsu masu jiran shari’a, suna cewa wannan na daya daga cikin matsalolin da kan haddasa fasa gidajen yari da mahara kan yi, inda cikin dubban fursunoni suka tsere cikin shekarar guda da ta gabata. Amma suna cewa ana kula da fursunonin da kyau.
Da na ziyarci babban gidan yari na Fatakwal, wanda aka tanadar don fursunoni kamar 1000, jami’ai sun shaida mani cewa adadin fursunoni da ke gidan, ya ninka adadin wadanda gidan zai iya dauka, kusan sau hudu.
Gidan yarin na Fatakwal na daya daga cikin wadanda ake kira ”gidajen yari masu cikakken tsaro.” Katafaren gini ne, mai doguwar katanga wadda aka yi wa rawani da murdaddiyar waya mai kaifi, ga kuma babban kyaure na karfe da kwado.
Ma’aikatan gidan yarin na kai kawo a ciki da wajen gidan, yayin da masu tsaron kofar ke sa ido da yin binciken kwakwaf ga duk wanda ya kawo ziyara, kafin a bar shi ya shiga. Haka kuma shiga da wayar salula haramun.
Hukumomi sun hana mu shiga kurkukun, wato dakunan da fursunoni ke rayuwa, domin daukar hoto ko ganin halin da daurarrun ke ciki.
A maimakon haka, sun nuna mana wasu daga cikin fursunonin, zababbu, wadanda ake koya wa sana’o’i kamar dinkin tela da kafinta, da gyaran gashi da kuma wadanda ke karatun jami’a a cikin gidan yarin.
Manufar wadannan ayyuka a cewar hukumomi, ita ce kyautata rayuwarsu idan daga bisani aka sako su, suka koma cikin al’umma.
To amma Patrick Moses, wanda a wannan gidan yarin ya yi zamansa na jarun, ya shaida wa BBC halin da daurarru ke ciki ta fuskar cunkoso a kurkukun na da munin gaske.
A cewarsa, babu sararin da mutum zai kwanta, ya yi barci har da juyi. Hasali ma, inji shi, a ”a wasu lokutan, ala tilas wasu ke kwana a ban-daki” saboda matsalar cunkoso a dakunan kwanan.
Tsohon fursunan, ya ce hatta zama a cikin dakin na da wuya, domin a wasu lokutan jera su ake yi manne da juna. A cewar Patrick, ba a ba su abinci yadda ya kamata, ba a kulawa da su yadda yakamata idan suka kamu da ciwo kamar zazzabin cizon sauro, ko kurarraji da dai sauransu.
Mata na kuka tana tuna mijinta
Fursunoni da dama da ma iyalansu, kan nuna shakku kan irin bayanai da hukumomi kan bayar kan halin da ake ciki a gidajen yari a kasar.
A ganin wasu, hukumomin ba su yin kokarin da ya kamata wajen kyautata gidajen yarin da kuma kula da daurarrun.
A wajen birnin Fatakwal, na gana da wata matashiyar uwa, mai suna Joy Mkpeanebari, a gidansu.
Mijinta, Mkpeanebari Ebadee, mai shekara 34, ya rasu a gidan yarin na Fatwakwal a watan Nuwamban 2021. An kama shi ne a 2018 lokacin wani samamen ‘yan sanda bayan rikici tsakanin kungiyoyin asiri.
An kama shi ne kwana uku kacal da haifar dansu daya tilo mai suna Desire.
Bai taba ganin dan ba, kuma dan bai taba ganinsa ba, domin lokacin da aka haifi yaron shi yana wurin aiki. Joy ta ce kafin kama mijin nata, shi mai gadi a wani kamfani ne.
Rungume da danta, tana zubar da hawaye, tana kuma nuna mani hoton mijin, Joy ta shaida mani cewa sau daya ta yi magana da shi ta waya – lokacin da yake tsare a gidan yari.
“Lokacin da ya kira ni a waya yayin da yake gidan yari, ya rarrashe ni, yana cewa kada in rika yin kuka, zai dawo ba da dadewa ba, amma bai dawo ba.
“Cikin murya mai sosa rai, ta ce tana tuna maigidan nata ”saboda yadda yake kula da ni, yana wasa da ni, yana nuna mani soyayya.”
Shekara uku mijin Joy ya kwashe a gidan yari, ba tare da an yi masa shari’a a kotu ba, har zuwa lokacin da ya mutu.
Ba a yi masa adalci ba, domin an kama shi kan laifin da bai aikata ba” kuma aka yi sandin mutuwarsa a gidan yari.
“Ba sakacinmu ne ke haifar da mace-macen fursunoni ba”
Hukumomin Najeriya sun tabbatar da cewa akan samu rasuwar fursunoni a gidajen yari. To amma jami’ai na musanta zargin cin zarafin fursunoni, da kuma sakaci da kan kai ga mutuwar wasunsu.
Mista Alex Oditah, kwanturolan gidajen yari mai kula da jihar Ribas, ya shaida wa BBC cewa idan aka samu mutuwar fursuna a gidan yari, ba wai hakan na nufin ba a kulawa da su ba ne.
Ya ce “Mutane kan mutu a ko’ina. Ba a gidan yari ne kawai mutane ke mutuwa ba.”
A cewar Mista Oditah, “yawancin mace-macen fursunoni da ake fuskanta, mace-mace ne da ba a iya kauce masu.”
Shugaban gidajen yarin ya kuma ce ana bai wa fursunoni ingantacciyar kulawa ta fuskar kiwon lafiya domin akwai likitoci a gidajen yarin.
Ya ce amma idan cututtuka suka fi karfin kulawarsu a gidan yari, bisa shawarar likita, sukan kai marasa lafiya asibiti na gwamnati inda ake da karin kwararru domin a yi masu jinya.
Babban jami’in gidajen yarin ya ce galibin fursunoni da kan mutu, ba a cikin gidan yari suke mutuwa ba. Suna mutuwa ne a asibiti sanadin cututtuka kamar kanjamau ko ciwon suga da makamantansu.
“Muna iya kokarinmu wajen kawo gyara”
Hukumomin Najeriya na cewa sun dage wajen ganin an inganta halin da gidajen yarin kasar suke ciki, jami’ai ke cewa sun damu matuka da halin da ake ciki. Sun ce suna kokarin inganta tsarin shari’a da hukunta laifuka ba tare da an zalunci wanda ake zargi ba.
Ko a watan Disamban da ya gabata, gwamnatin kasar ta kaddamar da shirin hanzarta shari’a ta hanyar na’ura daga nesa a gidan yari na Kuje da ke Abuja babban birnin kasar.
Ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola ya ce yana fatan za a fadada shirin zuwa karin gidajen yari domin taimakawa wajen rage cunkoso da ake fuskanta sanadin jinkirin tsarin shari’a.
Shi ma Mista Alex Oditah, kwanturolan gidajen yari mai kula da jihar Ribas, ya shaida wa BBC cewa “muna hada kai da bangaren shari’a, muna tuntubarsu, mu shaida masu cewa gidajen yarinmu na da cunkoso.”
Ya kara da cewa babban alkalin jihar na taimakawa wajen ziyartar gidajen yari a jihar don ganin halin da ake ciki, da kuma bukatar alkalai su rika kauce wa duk abin da zai sanya jinkiri a shari’a, da kuma sanya masu jiran shari’a dadewa a wakafi.
Mista Oditah ya ce wannan mataki ya taimaka wajen sako fursunoni da dama a gidajen yari a jihar, wato fursunonin da bai kamata a ce an ci gaba da tsare su ba.
Haka kuma hukumomi na cewa suna kokarin fadada ayyukan koyar da sana’o’i a gidajen yari domin kyautata rayuwar fursunoni da iyalansu.
To amma ga dubban fursunoni da kuma iyalansu wadanda suka yi imanin an zalunce su, duk wani yunkuri da za a yi, ko ake yi, zai kasance tamkar ihu bayan hari ne, za su dade suna jin radadin halin da suka shiga sanadin raunin tsarin na Najeriya.