Kungiyoyi a kano sun ce abin takaici ne yadda gwamnatin ta Kano ke amfani da majalisar dokokin jihar wajen samun damar karbo bashin, duk da irin matsin da zai jefa jihar a shekeu masu zuwa.
Cikin kungiyoyi masu fafutukar, akwai KAJA mai fafutukar ganin an kare hakkokin fararen hula a jihar ta Kano, wadda ke da ra’ayin gwamnatin jihar ba ta da hanyoyin samun kudaden shigar da za ta iya biyan su.
Kungiyar ta kuma yi kira ga sauran kungiyoyi da al’umomin jihar da su mike tsaye wajen kokarin da ta ke yi na ceto jihar daga kangin bashi.
Comrade Sa’id Dakata shi ne shugaban kungiyar KAJA mai fafutukar an kamanta gaskiya da adalci a ayyukan gwamnati a Kano, kuma ya shaida wa BBC cewa “Mu da muka nazarci ilimin tattalin arziki a makaranta da kuma wadanda muke mu’amulla da masu tafiyar da gwamnati, mun san cewa basussukan da ake karbowa ba alheri ba ne domin ba sai an karbo bashi za a iya yi wa jama’ar jihar aiki ba.”
Ya kuma ce “Irin basussukan da ake karbowa, ba a fayyace ainihin ayyukan da za a yi da su, shi yasa za ka ga abubuwa ba sa sauya zani.”
Da aka tambaye shi kimanin nawa gwamnatin Kano ta ciwo bashi daga waje, sai ya ce: “Ai lamarin ya wuce lissafi, domin kana cikin lissafta wanda ke kasa, sai ka ji an ce ga wasu biliyoyin za a karbo su. Abin da muka mayar da hankali a kai shi ne za mu rika garzayawa kotu kan dukkan bashin da ba mu gamsu da shi ba.”
Ya kuma ce “Ko bayan wannan gwamnatin ta sauka, sai mun kai wa EFCC bayanan da bincikenmu ya bankado kan basussukan da aka karbo. Duk wanda ya ci kudin al’ummar Kano da sunan bashi ya ci yadin mage, kuma kowa ya ci wannan yadin magen sai ya yi amansa.”
Wasu bayanani da ofishin da ke kula da basussukan da aka karba a Najeriya ya wallafa a shafinsa na intanet na watan Satumbar wannan shekarar na cewa jihar Kano na da bashin da ya kai Naira 102,351,644,358.62.
Shehu Na’Allah Kura, shi ne kwamishinan kudi na jihar Kano, kuma ya shaida wa BBC cewa jihar za ta biya wani kaso mai tsoka na bashin, kuma ya ce bai fi karfin ta biya shi kamar yadda wasu ke ikirari: “Misali akwai aikin samar da hasken lantarki a Tiga da gwamnatin jiha ke yi, kuma gwamnatinmu ta karbi bashin Naira biliyan 10 wanda tuni ta kusa biyansa.”
Ya kara da cewa duk bashin da aka karbo a jihar ana biyansa kamar yadda tsarin karbo shi ya nuna.
“Dukkan bashin da ya dace mu kammala biyansa a wa’adin mulkinmu, to in atabbatar maka cewa za mu biya shi baki dayansa,” in ji shi.