An bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da ya gargadi ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, kan zargin tsoratar da gwamna Sim Fubara. Rundunar ci gaban Neja Delta ta yi barazanar sanya bama-bamai idan Tinubu ya kasa gargadi Wike. Kungiyar tsagerun Neja-Delta ta ce ba za ta sake bari ana tursasa Gwamna Fubara a jihar Ribas ba.
Rundunar raya yankin Neja Delta ta yi barazanar rufe gidajen man fetur a yankin saboda yunkurin da ministan babban birnin tarayya, Byesom Wike ya yi na yiwa gwamnatin gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara ke yi.
Kungiyar tsagerun Neja Delta ta bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya gargadi Wike bisa zargin sa da alaka da Fubara na tsawon watanni.
Duba nan:
- Harin da Isra’ila ta kai ga iran ba guri 20 bane, karya ne
- IMF ta musanta cewa tana bayan cire tallafin mai
- Militant Group Threatens to Bomb Oil Installations, Details Emerge
Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, kakakin kungiyar Justin Alabraba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, 27 ga watan Oktoba.
“Tun watannin da suka gabata, Wike ya ci gaba da zagi da cin mutuncin Gwamna Fubara tare da yin tasiri a gwamnatin tarayya. Ba za mu sake jure hakan ba.”
Kungiyar ta bayyana fushin ta kan wani shiri da ake zargin Wike na dakatar da rabon kudaden kananan hukumomi ga jihar ta hanyar hukuncin da kotu ta yanke a ranar Litinin, 28 ga watan Oktoba.
Alabraba ya ce:
“Mambobin mu ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen rufe gidajen man fetur idan wani alkali a Abuja ya fitar da wata sanarwa da ta hana kananan hukumomin jihar Ribas aiki, ta hana su gudanar da aikinsu na jama’a.
“Za mu dauki mataki nan take. Za a mayar da martani cikin gaggawa, kuma za mu rufe manyan gidajen mai a yankin Neja Delta.
Idan har shugaba Bola Tinubu ya baiwa Wike damar kawo cikas ga harkokin mulki a kananan hukumomin jihar Ribas, mu ma za mu kawo cikas ga harkokin mulki a dukkan matakai.
Ba za mu iya ci gaba da shan wahala ba yayin da sauran sassan Najeriya ke ci gaba. Wike dole ne ya bar Fubara shi kadai.”