Wataƙila burin Peter Obi na neman zama shugaban ƙasa ya sami babban hamayya daga kungiyar mabiya Kiristanci.
Tsohon gwamnan Anambra na daya daga cikin ‘yan takarar da za su fafata a babban zaben da ke tafe.
Ƙungiyar matasan Kiristan, amma, ta bayyana Obi a matsayin wanda ba ya jure wa wasu addinai.
Kasa da kwanaki 100 kafin yin babban zaben shugaban kasa, an bukaci yan Najeriya su yi hattara da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Leadership ta rahoto.
Legit.ng ta tattaro cewa wata kungiyar matasan kirista mai suna United Christian Youth Forum of Nigeria (UCYFN) ke ta bada gargadin a Abuja, babban birnin tarayya, a ranar Juma’a 18 ga watan Nuwamba.
Kungiyar ta dage cewa Obi, ainihin halin tsohon gwamnan na jihar Abia ya banbanta da abin da ke ya ke ikirari a yanzu.
Da ta ke magana wurin taron manema labarai, kungiyar karkashin jagorancin Bro.
Peterson A Daniels a matsayin shugaba, ta zargi Obi da amfani da addini wurin rudar magoya bayansa da wasu yan Najeriya.
Ya ce:
“Kamar sauran yan Najeriya, an baza muku hotunan ziyarar da dan takarar shugaban kasar na Labour Party, LP, Peter Obi ya kai jihar Edo a matsayin kamfen dinsa na zaben shugaban kasa na 2023.
Cikin ziyarar akwai inda Mr Obi ya tsaya wurin addu’o’in dare da Mass na Katolika, inda aka gan shi ya durkusa limamin coci na masa addu’o’i a hotuna da suka bazu.
“Kafin fara kamfen, Obi ya rika ziyartar cibiyoyin ibada a kasar ta hanyar yarjejeniya da masu kula da wuraren da wakilansa suka yi.
An tallata wadannan ziyaran a kafafen sada zumunta da watsa labarai, don nuna dan takarar na LP a matsayin mutum mai tsoron Allah.”
Na Maka Magiya Dan Allah’ Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Roki Wike Ya Goya Masa Baya a 2023
Daniels ya ce ya zama dole su ankarar da yan Najeriya kada su yarda a rude su su goyi bayan wakilan “shedan a matsayin shugaban kasa na gaba.”
Ya kara da cewa tsananin kishin addini da Obi ke nunawa tun fitowar shi a matsayin dan takarar jam’iyyar LP ba komai bane illa face boye ainihin halinsa.
Shin Peter Obi ya tsani wadanda ba yan darikar Katolika ba da mabiya sauran addinai?
Kungiyar ta kuma kara da zargin Obi da kin jinin wadanda ba yan darikar katolika ba da mabiya wasu addininan a Najeriya, tana mai cewa dan takarar shugaban kasar na LP bai cancanci zama shugaban Najeriya ba a 2023.
Ya jadada cewa:
“A karshe, kungiyar Matasan Kirista ta Najeriya tana gargadi ga yan Najeriya da su yi hattara da dan takarar shugaban kasa Labour Party, Mista Peter Obi, wanda ya tabbatar wa yan kusa da shi cewa zai gudanar da gwamnatin Katolika idan aka kuskure aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.
“Zai hana Pentecostals, Protestants, Musulmai, Masu bautan dabobbi da Mulhidai daga amfana da romon dimokiradiyya kamar dai ba mutane bane.
Amma, koyarwarmu na Kiristanci ba ta nuna musgunawa kowa kan wadannan banbance banbancen ba.
Aikin da Yesu ya ba mu shine mu shaida wa duniya, wanda shine hanya mafi kyau don jawo su gare mu a maimakon bangaranci da Mr Obi ke yi.”
A bangare guda, Ohanaeze Ndigbo Worldwide, kungiyar yan kabilar Igbo, ta jadada goyon bayanta ga Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP.
Kungiyar tana da banbanci da Ohanaeze Ndigbo, karkashin jagorancin George Obiozor, The Cable ta rahoto.
Source:Legithausa