Kungiyar Malaman Masu Koyarwa ta Jami’o’i, ASUU, sun janye yajin aikin da suka kwashe wata takwas suna yi amma a kan sharadi.
Kungiyar malaman ta zauna taro da shugabanninta a sakateriyarta dake Abuja bayan an kammala na rassanta a ranar Laraba.
Kamar yadda aka sani, kotun daukaka kara ce ta umarci malaman makarantar da su koma aji kafin a cigaba da sauraron shari’ar su.
Kungiyar Malamai Masu Koyarwa ta Jami’o’i, ASUU, ta janye yajin aikin wata takwas da ta kwashe tana yi amma cike da sharudda.
Kamar yadda rahotannin da suka riski jaridar Vanguard suka bayyana, kungiyar ta janye yajin aikin ne bayan ganawa da shugabanninta a daren Alhamis wanda har suka kai sa’o’i farko na ranar Juma’a suna tattaunawa.
ASUU da ta janye yajin aikinta kafin a saurari shari’arsu ta daukaka karar da suka yi.
Mambobin kwamitin zartarwa na kasa wadanda suka hada da shugabannin rassan su da shugabanninsu na kasa sun halarci taron.
ASUU da aka yi a sakateriyarsu ta kasa dake Abuja. Idan za a tuna, kungiyar ASUU ta fada yajin aiki tun ranar 14 ga watan Fabrairun 2022, watanni takwas kenan cif.
Bayan shafe tsawon lokaci ana yajin aiki dalibai suna ta korafin ana bata musu lokaci da yawa sun fara sana’oi sakamakon tsayin da yajin aikin yayi yanzu an dawo makaranta burin dalibai ya cika.
Babbar barazanar da take fuskantar harkar ilimi a Najeriya bata wuce shakulatun bangaro da gwamnatoci kanyi da bangaren na ilimi ba, a ta bangare malaman jami’a kuma suna bukatar abubuwa da dama daga Gwamnati.
Source:legithausang