Kungiyar kwadago A Najeriya NLC Za Ta Fara Yajin AIkin Jan Kunne Na Kwana 3.
Rahotanni sun bayyana cewa babbar kungiyar kwadago ta kasa a Najeriya NLC acikin wata takadar bayan taro na hadin guiwa dake dauke da sa hannun shugaban Kungiyar ta kasa Ayuba Waba ta sanar da aniyarta na fara yajin aikin jan kunne na kwanaki 3 a fadin kasar don nuna goyon bayansu ga kungiyar malam Jami’oi ta kasa ASUU
Tun a ranar 13 ga watan Aprilu ne kungiyar ta NLC ta bawaya gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 21 da ta kafa kwamaitin da zai kawo karshen takddamar dake tsakaninta da kungiyar malam ta kasa wato Asuu da zai kawo karshen yajin aikin da suke yi, kana sun yi barazanar bin sahun kungiayr ta ASUU matukar gwamnati bata dauki mataki kan batun ba.
Haka zalika sun yi suka game da yadda matsalar rashin tsaro ta yi kamari a kasar, inda suka yi kira ga gwamnati da ta dauki matakin gaggawa wajen shawo kan matsalar tun kafin wankin hula ya kaita dare ya namae kasar baki daya, kana sun bukaci gwamnati da ta gaggauta kwato wadanda aka yi garkuwa dasu a lokacin harinn jirgin kasa Abuja zuwa Kaduna.
Daga karshe ya mika sakon taya murna ga dukkan Ma’aikata a fadin kasar na zagayowar ranar Ma’aikata ta kasa wato 1 ga watan mayu , kana ya sha Alwashin fitar da sanarwa da gaggawa idan aka samu canji game da ranar da za’a yi bukin ranar ma’aikata ta kasa a fadin kasar.