Kungiyar ta ”Amnesty International” wacce ta shahara da rajin kare hakkin dan adam a cikin gida najeriya dama sauran kasashen duniya tayi Allah wadarai da wasu kalamai wadanda ministan harkokin cikin gida Alhaji ra’uf aregbosola yayi.
Ministan na harkokin cikin gida dai a jawaban nasa yayi kira ga gwamnonin jihohi dasu gaggauta sanya hannu domin aiwatar da hukuncin kisa ga wasu fursunoni a najeriya.
Kungiyar wacce ta bayyanar da hakan a shafin ta na tuwita a ranar asabar 24 ga watan yuli ta bayyana kalaman ministan a matsayin wadanda suka sabawa dan adamtaka kuma da bukatar ya gaggauta janye su kuma ya nemi yafiyar ‘yan najeriya a matsayin sa na wanda yake rike ofishin al’umma.
Kungiyar ta bayyana cewa aiwatar da hukuncin kisa baya hana aikata laifi illah yana samar da take hakkokin al’umma kuma duk duniya tana bisa wannan tsari saboda hakanan babu bukatar a dinga yanke hukuncin kisa babu sanya lura a najeriya.
Kotunan najeriya dai sun shahara da tara masu laifi a kurkuku ba tare da hukunci ba wanda hakan ke zaman babbar matsala a tsarin tafiyar da shari’oi a fadin kasar ta najeriya.
A wani labari na daban kuma wani magidanci a jihar katsina ya canja ma diyar sa suna daga ”buhariyy” zuwa khausar.
Magidancin dai ya bayyana dalilan sa na canja suna diyar tasa wadanda suka hada da watsa masa kasa a ido da gwamnatin shugaba buhari tayi, inda ya bayyana cewa ya gwammace ya mayar da sunan diyar tasa khausar hakan zaifi domin dama kyakykyawan zaton da yake dashio ga shugaba buharin shine yasa ya sanya ma diyar tashi suna buhariyya amma yanzu tunda ta bayyana buhariyyar babju dadi domin gashi kowa yana ji a jikin sa saboda hakanan babu bukatar ya cigaba da barin sunan diyar tasa a sunan wanda yanzu bashi da ma’ana a ta bakin magidancin.