Kungiyar gwamnonin Nijeriya (NGF) ta roki gwamnatin Jihar Kaduna da kungiyar kwadago ta kasa (NLC) da su bi hanyar zaman lafiya wadda za su yi sulhu a tsakanin su.
Kungiyar wadda take karkashin shugabancin gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi , ya bayyana hakan ne a cikin sanarwar da aka fitar, bayan da kungiyar ta kammala taron a ranar Laraba.
“Game da rikicin ma’aikata a jihar Kaduna, kungiyar ta bada goyon bayan ta ga shi gwamnan Jihar Kaduna, a kokarin da yake na samarwa su ma’aikatan ingantacciyar rayuwa.
“ kungiyar abubuwan da suke faruwa a Jihar Kaduna ku san dukkan irin matsalolin ana samunsu a Jihohi, ta kuma yi kira ga dukkan gwamnoni da su maida kare rayuwar al’ummar su. Duk kuma wani matakin da za a dauka kada a wuce gona da iri.
“kungiyar ta yi kira da dukkan wadanda rikicin na Kadun ya shafa, da su yi kokari su kawo karshen takaddamar data shiga tsakanins, saboda matsalolin da wahalar basu kadai bane take shafa.
Ita dai wannan takin saka tsakanin shi gwamnan da ‘shugabannin kungiyyar ‘yan kwadago ya yi kamari ne sosai, inda suka fara yajin aikin gargadi na kwana biyar, a sanadiyar korar ma’aikatan da gwamnan ya yi.
kungiyar kwadago ta kasa ta dai jingine shi yajin aikin ne ranar Laraba bayan da aka samu sa bakin Ministan kwadago Chris Ngige, wanda ya bukaci dukkansu, suyi hakuri, domin da akwai wani matakin da zai taimaka wanda gwamnatin tarayya zata yi, a Abuja.
Gwaman El-Rufa’i ya tsokani ma’aikata inda yayi kokarin korar da dama daga cikin su kuma kungiyar tayi kokarin taka masa birki amma gwamnan ya kekasa kasa ya farmaki zanga zangar lumanar da suka shirya.
A alamu dai suna nuna gwamnonin sun fahimci ba zasu iya shiga fadan da gwamna el rufa’i ya taro da ma’aikatan ba shine suka nemi ya sulhunta da ma’aikatan domin kada ya jefa su a rigimar da basu shirya ba.