Kungiyar EU Za ta Kara yawan Iskar Gas Da Take Shigowa Da Shi Daga Najeriya.
Mataimakin Darakta Janar na kwamitin dake kula da sashin makamashi na kungiyar tarayyar Turai Mathew Baldwin ya fadi cewa kungiyar Tarayyar Turai tana cikin tsaka mai wuya game da Iskar Gas da suke bukata sakamakon mamayar da kasar Rasha ta yi wa Ukrain da kuma rashin tabbaaci A kasuwar Iskar gas dake zama a matsayin babbar barazana da ka iya kawo yanke samar da iskar gas baki daya
Mista Baldwin wanda ya kai ziyara birnin tarayyar Abuja ya bayyanawa manema labarai cewa kungiyar tarayyar Turai tana da kokarin karawa yawan iskar gas da take shigowa da shi daga Najeriya fiye da wanda take shigowa da shi a halin yanzu,
Najeriya tana samar da kashi 14 cikin 100 na Iskar Gas da kungiyar ta EU ke bukata yayin da kashi 60 daga cikin 100 na iskar gasar daka safarasu daga Najeriya suna zuwa kasashen turai ne.
Daga karshe ya nuna cewa daya daga cikin manufarsa zuwa Najeriya shi ne gano Gaskiya, kuma kngiayr EU za ta taimakawa Najeriya wajen ganin ta cimma burinta na samar da wadatacciyar wutar lantarki , ana sa ran bangarorin biyu zasu kara ganawa a Watan Augusta domin ci gaba da tattaunawa.