Kungiyar Enyimba da ke gasar Firimiyar Najeriya ta nada Finidi George a matsayin kocin ta.
Wasan sa na farko a hukumance a matsayin babban kocin Enyimba zai kasance wasan zagaye na biyu na gasar zakarun kungiyoyin Afrika ta CAF Confederation Cup da kungiyar Diambers FC daga Senegal a tsakiyar watan Oktoba.
George, wanda ya kasance fitaccen dan wasan tawagar Super Eagles ta Najeriya ya bugawa kasar tasa wasanni 62 cikin shekaru goma sha biyar.
Ya kuma taka rawa muhimmiya wajen lashe gasar cin kofin Afirka a 1994 da Najeriya ta yi, kuma ya wakilci kasar a gasar cin kofin duniya guda biyu a shekarun 1994 da 1998.
A matakin kungiya, George ya lashe kofin Zakarun Turai na UEFA tare da Ajax a shekarar 1995, kuma ya buga wa kungiyoyin Real Betis, da Real Mallorca.
Kungiyar Kano Pillars tace sabon dan wasanta kuma kaftin din tawagar kwallon kafar Najeriya Ahmed Musa zai buga mata wasan farko tun bayan komen da yayi mata ranar Lahadin nan dake tafe wato 16 ga watan Mayu.
Was ana baya bayan nan da Pillars ta fafata da Warri Wolves a birnin Warri an tashi ne kunnen doki wato 1-1.
Bayan buga wasanni 20 a. gasar Firimiyar Najeriya, a halin yanzu Akwa United ke kan gaba da maki 37, Kano Pillars ta 2 itama da maki 37, sai Kwara United ta 3 da maki 36, yayin da Rivers FC ke da maki 35.
A can kasa kuwa Ifeanyi Ubah ce ta 19 da maki 17, sai Adamawa United ta 20 da maki 12.