Shugaban Kungiyar Dalibai Ya Yayi Kira Da Uwar Gidan Shugaba Buhari, Da ta Yiwa Allah Ta Sa.
A Saki Dalibin Da Aka Kama An Gurfanar da Aminu A Gaban kotu kan Laifin Cin Zarafin Uwargida Aisha Buhari kafar Twitter .
Mutane Da dama Wanda Suka Da Yan Siyasa, Masu Tasiri A kafafen sadarwa Sunyi Kira da A Saki Aminu.
Kungiyar dalibai ta kasa (NANS) ta yi Allah-wadai da tsare Aminu Adamu bisa wani rubutu da aka yi a Twitter kan uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari.
Shugaban kungiyar, Usman Barambu ne ya fadin hakan a wata sanarwa da suka rabawa manema labarai wadda Leadership ta samu.
Sanarwar Ta Bukaci a sako dalibin jami’ar tarayya dake Dutse, jihar Jigawa ba tare da wani bata lokaci ba.
Ya kuma ba da sanarwar wata zanga-zangar da za a yi a fadin kasar a ranar Litinin, 5 ga Disamba, 2022 don matsa lamba dan ganin an sako Aminu.
Sanarwar ta kara da cewa, “A ci gaba da yunkurin da muke dashi na ganin nan tabbatar tare da kwatowa kowanne dalibi yanci, muna so mu sanar da shugabannin, masu fada aji, yan siyasa sarakuna da su saka baki dan ganin an sako wannan yaro.”
Sanarwa ta kara da cewa: “Ana sanar da ku matakin da shugabannin kungiyar daliban Najeriya da suka dauka na ci gudanar da zanga-zanga a fadin kasar,” in ji Baranbu.
Ya kara da cewa: “Mun yi tuntuba tare da neman an saki dalibin . kuma muna sanar da jama’a zamu fara wannan zanga-zangar a Jami’ar Tarayya Dutse a ranar Litinin 5 ga Disamba, 2022 a fadin kasar.”
Shugaban kungiyar ya ce za a gudanar da zanga-zangar dan sanar da shugaba Buhari da Sufeto Janar na ‘yan sanda Usman Alkali Baba kuma baza a daina zanga-zangar ba har sai an sako dalibin.
Idan dai za a iya tunawa, Aminu Adamu wanda dalibi ne a shekarar karshe a Sashen Kula da Muhalli da Dabbobi a Jami’ar Tarayya ta Dutse, Jihar Jigawa, an zargi shi da cin mutuncin Aisha Buhari.
Daga baya mai shari’a Halilu Yusuf na wata babbar kotun birnin tarayya ta tasa keyar sa a gidan yari na Suleja da ke jihar Neja bisa laifin.
Source:LegitHausa