Kungiyar Boko Haram da ke Najeriya ta tabbatar da mutuwar shugabanta Abubakar Shekau wanda majiyoyi suka ce ya mutu ne sakamakon rikici tsakaninsa da bangaren ISWAP da ke adawa da jagorancinsa.
Wani faifan bidiyo da sabon kwamandan kungiyar Bakura Modu ya fitar da harshen larabci ya bukaci kwamandodin bangaren dake adawa da jagorancin Abubakar Shekau da su cigaba da biyayya duk da rashin shugaban nasu wanda ya mutu a watan jiya.
Masu sa ido kan rikicin kungiyar na kallon mutuwar Abubakar Shekau a matsayin wadda zata bude sabuwar kofa a rikicin, sakamakon tasowar kungiyar ISWAP da kuma illar da take cigaba da yiwa jama’a a yankin arewa maso gabas.
Faifan bidiyon da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya samu daga wata majiya kusa da kungiyar boko haram da Bakura Modu na tabbatar da cewar har yanzu rikicin cikin gida tsakanin bangarorin bai kare ba.
Shekau wanda yayi kaurin suna lokacin da ya kwashi daliban makarantar mata kusan 300 a Chibok a shekarar 2014 ya hallaka kan sa a watan jiya maimakon mika kan sa lokacin da kungiyar ISWAP ta masa kofar rago.
Wata muryar da aka nada ta jiyo kwamandan ISWAP Abu Musab Al-Barnawi na tabbatar da mutuwar Shekau lokacin da ya hallaka kan sa yayin arangama da mayakan su.
Bidiyon da ba’a sanya lokacin da aka nade shi ba ya nuna Bakura tare da mayakan sa dauke da makamai lokacin da yake jawabi a gaban na’urar daukar hoto, yayin da Yan bindigar ke tsaye kusa da shi.
Bakura na daga cikin kwamandodin kungiyar boko haram dake kai hare hare a Yankin Tafkin Chadi inda ake fama da matsalar tsaro akan iyakokin yankin.