Kungiyar ASUU A Najeriya Ta Bayyana Dalilanta Na Shirin Sake Tsunduma Yajin Aiki.
Kungiyar malaman Jami’oi a Najeriya Asuu ta bayyana cewa majalisar zartarwar kungiyar za ta gudanar da wani taro a jami’an legas a ranakun 12-13 na watan fabareru da muke ciki domin sake bitar irin matakin da za su dauka kan shirinta na shiga yajin aiki har sa an share musu hawaye
Ta kara da cewa idan har gwamnati tarayya bata dauki matakin gaggawa kan batun ba, to ko shakka babu malaman za su shiga yajin aikin da sai baba ta gani,
Ita dai kungiayr Asuu tana bukatar gwamnatin tarayya ta yi aiki da yarjejeniyar da aka rattaba hannun akai,a shekarar da ta gabata.
Anasa bangaren shugaban Jami’an jihar kwara Dr Lau Sheu ya fadi cewa gwamnati na kokarin kaucewa aiki da nauyin day a rataya a wuyanta ta hanyar sanya ministoci su sa ido kan yadda za’a aiwatar da yarjejeniyar da aka rattaba hannu akai.