Kun san mutum 18 da ke takarar shugabancin Najeriya?
Hamza al-Mustapha (AA)
Hamza al-Mustapha, tsohon babban jami’in tsaro ga shugaban soji lokacin Janar Sani Abacha.
Bayan mutuwar Abacha, an ɗaure shi tsawon sama da shekara 10 kan kisan matar Moshood Abiola, Kudirat.
Sai da ya kayar da wani ɗan takara gabanin ya samu damar takara a ƙarƙashin jam’iyyar AA, wato Action Alliance.
Johnson Chukwuka yake masa mataimaki.
Omoyele Sowore (AAC)
Omoyele Sowore, shi ne mai jaridar nan ta intanent da ke Amurka, da ake kira Sahara Reporters.
Ya fito takarar ce a karo na biyu bayan wadda ya yi a 2019.
An kama shi a bara lokacin da suka yi gangamin zanga-zangar “Revolution Now” wadda ya so ta karaɗe ko ina a Najeriya.
Yana takara ne a ƙarƙashin Jam’iyyar African Action Congress (AAC) tare da Magaji Garba, a matsayin mataimakinsa.
Dumebi Kachikwu (ADC)
Dumebi Kachikwu, ɗan kasuwa ne, kuma shi ne mai gidan talabijin ta Local Roots.
Yana takara a jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), tare da Buhari Ahmed, a matsayin mataimakinsa.
Sani Yusuf (ADP)
Ɗan siyasa ne kuma ɗan kasuwa daga arewa maso yamma a jihar Kano, yana da shirin kawo “karshen cin hanci” a Najeriya.
Yana takara ce a Action Democratic Party (ADP) tare da mataimakinsa Udo Okoro.
Bola Tinubu (APC)
Bola Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas ne da ke kudu maso yammaci.
Ya yi sanata na wani lokaci a farkon shekarun 1990, wannan ne karon farko da yake takarar shugaban ƙasa a jam’iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC).
Kashim Shettima, tsohon gwamnan jihar Borno ne ke yi masa mataimaki.
Peter Umeadi (APGA)
Shi ne tsohon alkalin alƙalan jihar Anambra, Peter Umeadi, yanzu Farfesa ne a fannin shari’a.
Yana wakiltar All Progressives Grand Alliance (APGA), Mohammed Koli ne abokin takararsa.
Nnadi Osita (APP)
Nnadi Osita, yana takara ne tare da Hamisu Isah a jam’iyyar Action Peoples Party (APP).
Ojei Chichi (APM)
Ojei Chichi, ita ce mace ɗaya ‘yar takarar shugabancin Najeriya a zaɓe mai zuwa, tana takara ne a jam’iyyar Allied People’s Movement (APM).
Ibrahim Mohammed, wani ɗan siyasa daga jihar Delta da ke kudanci shi ne mataimakinta.
Christopher Imumolen (AP)
Christopher Imumolen farfesa ne a fannin tsangayar nazarin injiniyanci.
A matsayinsa na ɗan shekara 39, shi ne ɗan takara mafi ƙarancin shekaru a bana.
Suna takara tare da Bello Maru a jam’iyyar Accord Party (AP).
Adenuga Oluwafemi (BP)
Adenuga Oluwafemi yana takara ne a jam’iyyar Boot Party (BP), tare da Mustapha Turaki a matsayin mataimakinsa.
Peter Obi (LP)
Tsohon gwamnan jihar Anambra da ke kudu maso gabas, Peter Obi shi ne dan takarar shugaban ƙasar jam’iyyar Labour Party (LP).
Wannan ne karo na biyu da yake takara. Karon farko shi ne ya yi wa Atiku Abubakar mataimaki a 2019 karkashin jam’iyyar PDP.
Rabiu Musa Kwankwaso (NNPP)
Rabiu Kwankwaso tsohon gwamnan jihar Kano ne. Ya yi gwamna har sau byu, ya yi sanata tsakanin 2015 da 2019.
A baya an zaɓe shi, a matsayin ministan tsaro.
Wannan ne karo na uku da yake neman babban ofishi. Takararsa biyu da ya yi a baya duka faduwa ya yi a zaɓen fidda gwani.
Yana takara ne da mataimakinsa Odiri Idahosa a jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP).
Okwudili Anyajike (NRM)
Okwudili Anyadike ya samu damar takara ne bayan kayar da abokin hamayyarsa na kusa da ya yi a jam’iyyar NRM.
Yana takara ne tare da Kyabo Muhammad a matsayin mataimaki.
Kola Abiola (PRP)
Kola Abiola ɗa ne ga hamshaƙin ɗan kasuwar nan kuma ɗan siyasa Moshood Abiola, wanda aka ɗauka a matsayin wanda ya lashe zaɓen 1993 wanda gwamnatin soji ta soke.
Shi ma ɗan kasuwa ne tamkar mahaifinsa, suna takara ne tare da Zego Haruna a jam’iyyar People’s Redemption Party (PRP).
Atiku Abubakar (PDP)
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar yana wannan takarar ne a karo na shida.
Ya yi wa’adi biyu a matsayin mataimakin shugaban shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo.
Gwamnan jihar Delta da ke yankin kudancin Najeriya Ifeanyi Okowa, shi ne ke yi masa mataimaki a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Adebayo Adewole (SDP)
Adebayo Adewole lauya ne, ɗan kasuwa ne kuma ɗan siyasa ne a jihar Ondo.
Yana takara ne a jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), tare da abokin tafiyarsa Buhari Yusuf.
Malik Ado-Ibrahim (YPP)
Malik Ado-Ibrahim yarima ne a yankin tsakiyar Kogi kuma shi ne mai kamfanin makama shi na Bicenergy.
A 2020, yana cikin labaran auren auren Adama Indimi, ‘yar gidan biloniyar ɗan kasuwar nan mai harkar mai da kuma taimako Mohammed Indimi.
Yana takara a jam’iyyar Young Progressives Party (YPP), Enyinna Kasarachi ne mataikamakinsa.
Daniel Nwanyanwu (ZLP)
Daniel Nwanyanwu shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar Zenith Labour Party (ZLP) kuma shi ne shugabanta na ƙasa.
Abubakar Ramalan ne yake yi masa mataimaki.