Bayan kiraye-kirayen da aka yi na soke shirin nan na bautar kasa (NYSC), kudurin dokar da ke neman tabbatar da hakan ya tsallaka karatu na biyu a Majlisar Wakilai ta Tarayya.
Kudirin wanda yana cikin gyaran da ake yi wa Kundin tsarin mulki na tarayyar Nijeriya na 2020, an gabatar da shi a majalisa wanda har ya samu karatu na biyu kuma ya tsalla. Mista Awaji-Inombek Abiante ya gabatar da kudurin a zauren majalisar a cikin bayanin shawarar da ya gabatar, inda ya zayyana dalilai daban-daban da za su sa a soke NYSC.
Wani bangare na bayanin na cewa cewa, “wannan kudirin yana neman a soke sashi na 315 (5) (a) na kundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya na shekarar 1999 wanda aka yi wa kwaskwarima a kan wadannan dalilai.
“Kisan gilla ga mambobin bautan kasa da ba su ji ba ba su gani ba a wasu sassan kasar saboda ta’addancin ‘yan bindiga, tsattsauran ra’ayin addini da rikicin kabilanci, yawan sace-sacen mambobin bautar kasa da ake yi a fadin kasar.
“Hukumomi da ma’aikatu na gwamnati da masu zaman kansu sun daina daukar matasa kwararrun ‘yan Nijeriya aiki, saboda ana tura musu ‘yan bautan kasa.
“Don haka sun dogara kacokan kan samuwar ‘yan yi wa kasa hidiman da ba a biyansu albashi mai tsoka kuma ake watsar da su ba tare da cimma komai ba a karshen shekarar su ba tare da fatan samun aiki ba.
“Saboda rashin tsaro a duk fadin kasar nan, yanzu haka hukumar kula da bautar kasa ta fara tura ‘yan bautan kasa yankinsu, don haka ya saba daya daga cikin manufofin kafa kungiyar, watau bunkasa alakar da ke tsakanin matasan Nijeriya da inganta kasa da hadin kai da hadewa wuri guda.”
Yanayin dai yazo ma ‘yan najeriya da mamaki duba da yadda kudurin tabbatar da aikin yiwa kasa hidima din ke zaman wata hanya ta samar da zumunci tsakanin ‘yan najeriyar.