Kotun Sojoji da ke zamanta a Abuja, a ranar Talata, ta yanke wa Manjo Janar U. M. Mohammed hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari.
Shugaban kotun sojin, Manjo Janar James Myam, ya samu babban hafsan sojin da laifuka 14 cikin 18 da ake tuhumarsa da aikata wa.
Babban hafsan da aka yankewa hukuncin zai mayar da dalar Amurka $217,900 da kuma Naira Biliyan N1.65bn ga kamfanin da ke kula da kadarorin rundunar sojin Nijeriya.
Hukuncin zai tabbata ne in kwamitin majalisar sojin ta zartar da hukuncin.
A wani labarin na daban gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sanar da daukaka darajar kwalejin Mustapha Umar Elkanemi ta karatun Larabci da ke Maiduguri zuwa wata babbar cibiya ta musamman ta koyar da ilimin larabci da ilimin addinin Musulunci domin yaki da irin fahimtar da ‘yan ta’addan Boko Haram suka yi wa Karatun Addinin Musulunci.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata a yayin da ya kai ziyarar duba kwalejin domin shirye-shiryen sauya tsarin kwalejin.
Wannan tsarin dai, an yi shi ne da nufin dakile irin fahimtar da kungiyar Boko Haram ta yi wa addinin Musulunci. Kungiyar ta yi kaurin suna wajen tsaurin ra’ayi da ikirarin da’awar addinin Musulunci da kafa gwamnatin musulunci sabida sabanin fahimtar karantarwar addinin.
“Idan aka kafa sabuwar cibiyar, za ta kasance karkashin karantarwar Jami’ar Al-Azhar da ke birnin Alkahira ta Misra kuma za ta dinga ya ye daliban da za a tura su kananan hukumomin Borno 27 domin yin wa’azin da zai dakile akidar Boko Haram.”
Don haka, Gwamna Zulum ya umurci sabuwar hukumar ilimin Larabci da Tsangaya da aka kafa ta jihar Borno da ta karbi ragamar tafiyar da dukkanin makarantun Tsangaya da na islamiyya a jihar Borno.
Source LEADERSHIPHAUSA