Kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar Kebbi ta fara sauraron kararrakin da aka shigar a gaban kotun a ranar Laraba a Birnin Kebbi, babban birnin jihar.
An fara zaman ne tare da kara mai lamba EPT/BK/HR/02/2023 cewa Muhammad Bala Usman yana kalubalantar sakamakon zaben mazabun Yauri/Shanga da Ngaski a kotun.
Yayin da koken ya nuna cewa Muhammad Bala Usman da jam’iyyar PDP ne suka shigar da karar wadanda ake karar su ne Hon. Yusuf Tanko Sununu a matsayin wanda ake kara na farko, sai Jam’iyyar APC a matsayin na biyu sai kuma hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a matsayin mai na uku a cikin karar.
Lauyan masu kara, Barista Cif Magnus Ihejirika, ya tabbatar wa kotun cewa koken nasu ya balaga tun da aka yi musayar ra’ayi ma’ana yanzu an hade al’amura, don haka a shirye suke su ci gaba da gudanar da koken da suka shigar a gaban kotun.
Lauyan da ake kara na farko Barista Hussaini Zakariya SAN, Lauyan mai kara na biyu Barista Buhari Shehu da lauya na uku Barista M H. Hassan duk sun tabbatar wa kotun cewa yanzu maganar ta shiga.
Kotun da ke karkashin shugabancin Honourable Justice Margret Opara ta dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar Juma’a 28 ga watan Afrilu domin ci gaba da sauraren karar biyo bayan bukatar da lauyan masu shigar da kara Barista Cif Magnus Ihejirika ya gabatar na bukatar ya daidaita gidan nasu, da kuma lauyoyin masu ba da kariya na daya, na biyu da na uku, sun bayyana wa kotun cewa ba su da wata jayaya ko adawa ga bukatar da lauyan masu shigar da kara ke neman a dage zaman.