Kotun koli ta tabbatar da Ademola Adeleke a matsayin sahihin dan takarar gwamnan PDP a zaben fidda gwani.
An kai ruwa rana a PDP a jihar Osun tun bayan da aka samu rabuwar kai a zaben fidda gwanin da aka yi a jihar.
A yau dai kotun koli ta kawo karshen cece-kuce da ganin ni ke da gaskiya tsakanin ‘yan takarar da suka fito.
Kotun koli a ranar Alhamis 29 ga watan Satumba ta tattara da zababben gwamnan jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke a matsayin sahihin dan takarar da ya lashe zaben gwamnan jihar a zaben ranar 16 ga watan Yulin bana, Vanguard ta ruwaito.
Babbar kotun ta yi zama tare da alkalai biyar, inda ta kori karar da Prince Dotun Babayemi ya daukaka don kalubalantar Adeleke a matsayin sahihin dan takarar gwamnan PDP.
Idan baku manta ba, an yi zabe a bangarori biyu na jam’iyyar PDP a jihar Osun gabanin zaben da aka yi a watan Yuli.
Lauyan mai shigar da kara, Mr Adebayo Adelodun (SAN), ya janye karar ne bayan da kwamitin alkalai karkashin jagorancin Amina Augie, ya ja hankalinsa kan cewa shari’ar ba ta da makama.
Kwamitin ya tabbatar masa da cewa karar ba ta da wani sahihanci, inda ta jaddada cewa an shigar da karar kwanaki 14 bayan ka’idar da doka ta tanada, haka nan Daily Sun ta ruwaito.
An sha samun matsalolin rashin fahimtar juna a jam’iyyun siyasa a Najeriya, lamarin da ka iya zuwa har gaban kotu tare da neman alkalai su raba gardamar da ta kunno kai.
A wani labarin, rikicin ko wanene zai zama dan takarar sanatan da hukumar zabe ta INEC ta amince dashi a APC a mazabar Yobe ta Arewa ya kawo karshe, domin an zabi Bashir Machina a matsayin dan takara.
Wata babbar kotun tarayya karkashin jagorancin Fadima Murtala Aminu ta yanke hukunci a yau Laraba 28 ga watan Satumbam inda ta umarci INEC ta amince da Machina a matsayin dan takarar sanatan APC daga Yobe ta Arewa.
Tikitin takarar dai an jima ana kai ruwa rana akansa tsakanin Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawa da Bashir Bachina tun bayan kammala zaben fidda gwanin APC.
Source:legithausang