Kotu mafi girma a Najeriya ya shiga lamarin ranar daina da amfani da tsaffin takardun Naira.
Kotun koli ta yanke hukuncin wucin gadi kan bukatar da wasu gwamnonin Arewa suka shigar.
An dakatad da yunkurin haramta amfani da tsaffin takardun kudi ranar 10 ga Febrairu, 2023.
A yau Laraba, kotun kolin Najeriya ta dakatad da yunkurin da gwamnatin tarayya ke yi na hana amfani d atsaffin takardun Naira fari da ranar 10 ga Febrairu, 2023.
Kwamitin Alkalan kotun guda bakwai karkashin jagoranicin Justice John Okoro, ya dakatad da shirin bisa karar da wasu gwamnonin Arewa uku suka shigar kotun, rahoton ThisDay.
Gwamnonin uku sun bukaci kotun ta dakatad da shirin hana amfani da tsaffin takardun Naira da gwamnatin tarayya da babban bankin tarayya CBN ke kokarin yi a ranar 10 ga Febrairu, 2023.
Lauyan masu kara, Mr A. I Mustapha, SAN, ya bukaci kotun ya amince da bukatarsu saboda jin dadin al’ummar Najeriya. Ya bayyana cewa wannan doka ta gwamnati ya jefa yan Najeriya halin kakanikaye.
Ya ce yan Najeriyan da basu da lalitan banki sun kai kashi 60%, hakan bisa rahoton bankin CBN da kanta.
Lauyan ya kara da cewa muddin kotun koli bata shiga lamarin ba Najeriya na iya shiga wani irin hali saboda bankuna har sun fara rufe ofishohinsu.
Hukuncin Alkali Alkali Okoro yayin yanke hukunci ya ce bayan kyakkyawan dubi cikin lamari, zata amince da bukatar gwamnonin.
Yace: “An bada umurnin wucin gadi na dakatad da gwamnatin tarayya da bankin CBN or bankuna daga daina amfani fa takardun kudi 200, 500, 1000 a ranar 10 ga Febrairu, 2023 har sai an zauna kan lamarin an yi hukuncin karshe.”
Alkalin ya dage zaman zuwa ranar 15 ga Febarairu, 2023 domin sauraron karar. Buhari ya kira taron gaggawa na dukkan tsaffin shugaban kasa
A wani labarin kuwa, Shugaba Muhammadu Buhari ya kira taron gaggawa na majalisar magabatar Najeriya domin tattaunawa kan abubuwan da suka shafi tsadar man fetur, karancin Naira, rashin tsaro da sauransu yayinda ake shirin zaben 2023
Source:LegitHausa