Kotun daukaka kara da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta sallami shugaban haramtaciyyar kungiyar Indigenous People of Biafra, IPOB, Nnamdi Kanu, Channels Television ta rahoto.
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta gurfanar da Kanu ne a babban kotun tarayya da ke Abuja kan tuhume-tuhume 15 masu alaka da cin amanar kasa da ta’addanci da ta ke zargin ya aikata yayin fafutikan neman ballewa daga Najeriya.
Kotun Daukaka Kara Ta Sallami Nnamdi Kanu, Ta Kallubalanci Babban Kotu.
Kotun ta ce tuhume-tuhume 15 da aka yi wa Kanu bai bayyana wuri, rana, lokaci da yanayin laifukan da ya aikata ba kafin a dawo da shi Najeriya ba bisa ka’ida ba, tare da saba dokokin kasa da kasa.
Kotun ta kara da cewa gwamnatin tarayya ta gaza bayyana inda aka kama Nnamdi Kanu duk da irin manyan zargin da ta ke masa. Dakaci karin bayani …
A wani labarin na daban, Ana zargin jami’an sojoji da kai mamaya wani yanki na garin Mgbowo da ke karamar hukumar Awgu a jihar Enugu.
An tattaro cewa sojojin da ba a san dalilinsu na kai farmakin ba sun kona gidaje da dama.
Sun kai harin ne da sassafe inda suka ta harbi a sama lamarin ya sa mazauna yankin tserewa cikin dazuzzuka.
Rahotanni sun kawo cewa dakarun sojoji sun farmaki wani yanki na garin Mgbowo da ke karamar hukumar Awgu a jihar Enugu.
Sahara Reporters ta rahoto cewa lamarin ya haifar da rudani da fargaba a tsakanin al’umma yayin da mazauna yankin suna tsere cikin dazuzzuka mafi kusa.
Ana Zargin Sojoji Da Mamaye Wani Yanki
Wani mazaunin garin, Clement Ogonna ya fada ma Sahara Reporters cewa al’ummar kauyen sun wayi gari da karar harbi, wanda yace suna ta dira kan rufin kwano kamar saukar ruwa.
Ya ce: “Yayin da al’ummar kauyen ke gudun tsira, sojojin sun yunkura zuwa harabar Urulor a unguwar Okegu sannan suka kona gidaje.
“Bayan sun kona wani gini a unguwar Okegu, sai suka garzaya unguwar Ogudu inda suka kona gidaje uku kafin suka koma Isingwu.
“Yanzu haka da muke magana, sojoji na kona gidaje a Isungwu; kana iya hango hayaki yana tashi a sama.”
Ya ci gaba da cewa babu wanda zai iya cewa ga dalilin sojojin na kai masu farmaki.
A wani labarin, an tsinci matar wani malamin addini mai suna Adolphus Odo kwance a mace tare da yaranta biyu da kuma kannenta biyu a Amutenyi, da ke Obollo-Afor, karamar hukumar Udenu ta jihar Enugu a ranar Asabar.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa karar kararrawar agogo ce ta ankarar da makwabta inda suka fasa kofar kawai sai suka tsinci mutanen su biyar kwance babu rai a jikinsu.
Da yake tabbatar da lamarin, shugaban karamar hukumar, Solomon Onah, ya ce labarin ya jefa yankin karamar hukumar cikin alhini.