Kotun ɗaukaka ƙara ta soke tikitin Nuhu Damburam a matsayin ɗan takarar Sanatan Kano ta tsakiya karkashin PDP.
Kotu mai zama a Birnin Kano ta tabbatar da sahihancin zaɓen tsagin Sagagi wanda ya samar da Laila Buhari.
Alkalin Kotu yace bai kamata babbar Kotun tarayya ta kori karar ba tun farko bisa hujjar tsarin NJC wanda ke ƙasa da kundin mulkin ƙasa.
Kotun ɗaukaka ƙara dake zama a birnin Kano ta rushen zaɓen Danburam Nuhu a matsayin ɗan takarar Sanatan Kano ta tsakiya a inuwar jam’iyyar PDP.
Jaridar Daily Nigerian tace nan take Kotun ta tabbatar da halascin zaɓen fidda gwanin da tsagin PDP karkashin Shehu Sagagi ya gudanar, wanda ya samar da Laila Buhari a matsayin yar takara.
A ranar 26 ga watan Satumba, 2022, babbar Kotun tarayya mai zama a Kano ta sallami ƙarar saboda ba ta da hurumin sauraro domin an shigar da ƙarar a reshen Kano maimakon Abuja.
A cewar Kotu haka ya saɓa wa dokar ɓangaren shari’a na ƙasa (NJC) game da batutuwan da suka shafi zaɓe, kamar yadda jaridar Aminiya ta tabbatar.
Amma a hukuncin da Alƙalin Kotun ɗaukaka ƙara, mai shari’a Ita Mbaba ya yanke ranar Laraba, ya jingine matakin Kotun tarayya, inda yace ta tafka kuskuren game da Kes ɗin.
A zaman Kotu, ta bayyana cewa game da batutuwan dake biyo bayan zaɓe, dokokin babbar kotun tarayya da kuma kundin tsarin mulki 1999 da aka yi wa garambawul sun rinjayi tsarin NJC da kotun ta kafa hujja da shi.
Bayan haka, Kotun ɗaukaka ƙarar ta umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta cire sunan Danburam, ta maye gurbinsa da Laila Buhari.
A wani labarin kuma Kotu ta ɗaukaka kara dake zama a Yola, jihar Adamawa ta tabbatar da ɗan takarartakarar gwamnan jihar Taraba na APC.
A watan Satumban da ya gabata, babbar Kotu ta tarayya mai zama a Jalingo ta ruhse zaben fidda gwanin da ya samar da Sanata Bwacha a matsayin ɗan takarar APC.
Amma a hukuncin Kotu din ɗaukaka kara yau Alhamis, ta jingine hukuncin baya tare da tabbatar da halascin zaben.
Source:Legithausa