Kotun a Cote d’Ivoire ta zartas da hukunci daurin rai-da rai ga tsohon Firaministan kasar, kuma tsohon madugun ‘yan tawayen kasar Guillaume Soro dake gudun hijira, sakamakon laifin yunkurin wargaza kasa.
Baya ga Guillaume Soro, kotun ta kuma yanke hukuncin ga wasu daga cikin mukaraban sa da ake zargi da hada baki da tsohon Madugun ‘yan tawayen kasar, wandada aka kuma yankewa hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari.
Sai kuma wasu daga cikin sojojin kasar 7 da kotun ta samu da laifin tada tarzoma, wadanda kuma ta yankewa hukuncin daurin watanni 17 ko wannensu.
A wani labarin na daban mahukunta a Chadi, sun sanar da cafke wasu ‘yan asalin kasar Rasha da kuma Lithuania akalla 10, a yankin Laya-Fargeau mai fama da ayyukan tawaye a arewacin kasar.
Sanarwar da mahukuntan kasar suka fitar ta bayyana cewa, mutanen sun isa kasar Kamaru ne a ranar 25 ga watan Mayun da ya gabata, kafin daga bisani su tsallaka iyakar kasar Chadi ta hanyar amfani da mota.
Su dai ‘yan asalin kasar ta Rasha da kuma Lithuania, sun ce sun shiga yankin na Laya-Fargeau ne domin yawon bude ido, to sai dai tun jimawa mahukunta suka haramta kai ziyara a cikinsa, lura da yakin da ake fafatawa tsakanin ‘yan tawaye da kuma dakarun gwamnati.
An dai kwace kayayyaki da dama daga hannun mutanen, da suka hada da fasfo, wayoyin tarho, na’urorin kwamfuta da dai sauransu, kuma yanzu haka ana tsare da su ne a wani kasaitaccen otel da ke birnin Ndjamena.
A wata wasika da ta aika wa jakadan Rasha a birnin Ndjamena, Ma’aikatar Harkokin Wajen Chadi ta ce, ana tsare da mutanen ne saboda kare lafiyarsu, lura da cewa yankin da aka kama su na da matukar hadari.