Bayan kama ta da laifin kisan kai, Kotu ta yanke wa yar aikin marigayya mahaifiyar tsohon gwamnan jihar Edo hukuncin kisa.
Alƙalin Kotun ya ce hujjojin da aka gabatar masa ya tabbatar da cewa yar aikin ce ta kashe uwar ɗakinta Madam Igbinedion Bayanai sun nuna cewa matashiyar yar shekara 25 a duniya ta amsa laifinta kuma ta faɗi yadda ta aikata kisan kan.
Babbar Kotu a jihar Edo ta yanke wa yar aiki, Miss Dominion Okoro, yar shekara 25 hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan kama ta da laifin kashe mahaifiyar tsohon gwamn Edo, Lucky Igbinedion.
Tribune Online ta ruwaito cewa Alƙalin Kotun, Mai Shari’a Efe Ikponmwoba, shi ne ya ayyana hukuncin bayan tabbataar da laifin yar aikin wacce ta kashe Madam Maria Oredola Igbinedion da kujera mara abun jingina.
Bayanai sun nuna cewa matashiyar yar aikin ta yi ajalin uwar ɗakinta da nufin sace kuɗi N100,000 a ranar 1 ga watan Disamba, 2021 a gidanta da ke Ugbor, Benin City.
Alƙalin ya ƙara da bayyana cewa yar aikin bayan kashe uwar ɗakinta Madam Igbinedion, ta yi amfani da auduga ta toshe wa gawar kofofin hanci, daga bisani ta kira motar taxi don ta tsere washe gari.
Yar aikin ta amsa laifinta tun a hannun yan sanda Tun farko matashiyar ta amsa laifinta a hannun yan sanda da cewa ta yi amfani da ganye mai bugarwa wajen yi wa mamaciyar girki domin ta rasa karsashinta, ita kuma ta aiwatar da nufinta ba tare da wahala ba.
Alkalin ya ce duba da hujjar da Likitoci suka bayar na sanadin mutuwar matar, kwararan hujjojin da masu shigar da ƙara suka gabatar wa Kotu da karin amsa laifinta da ta yi, sun isa Kotu ta tura yar aikin a rataye ta.
Babbar yar uwar matashiyar mai suna Patience Okoro, ta tsallake haɗuwa da mai rataye wa bayan Kotu ta ayyana cewa babu hujjar da ta nuna tana da hannun a lamarin.
Ta ce abu ɗaya da ya haɗa Miss Okoro da ƙanwarta da ta aikata ɗanyen aikin shi ne ta kirata a waya ta sanar mata da cewa ga abin da ta aikata, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
A wani labarin kuma Gwamna Matawalle ya ceto mutane 3,000 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a Zamfara Gwamnatin jihar Zamfara karƙashin Bello Matawalle ta bayyana ɗumbin nasarorin da ta samu a ɓangaren tsaro tun farkon zuwanta.
Kwamishinan labarai, Ibrahim Dosara, ya ce daga 2019 zuwa yau gwamnati ta kub utar da dubbannin mutane daga hannun masu garkuwa.