A yau Alhamis, Sanata Ike Ekweremadu, da matarsa sun gurfana a gaban Kotu Majistire ta ƙasar Birtaniya kan zargin yanke sassan jiki.
Bayan tafka muhawarawa tsakanin ɓangarori biyu, Kotu ta yanke cewa wanda ake shari’ar kansa, shekarunsa 21 ba 15 bane Ta kuma ɗage zaman zuwa 4 ga watan Agusta, 2022 kuma ta maida Kes ɗin Kotun manyan laifuka.
Kotu ta ɗage zaman shari’ar tsohon mataimakin shugaban majalisar Dattawa, Sanata Ike Ekweremadu, da matarsa, Beatrice zuwa ranar 4 ga watan Agusta, 2022.
An sake gurfanar da ma’auratan a gaban Kotun Majistire Westminster bisa tuhumar yanke sassan jikin mutum ranar Alhamis, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. Gavin Irwin, shi ne lauya mai kare Sanata Ekweremadu, yayin da Szilvia Booker, ke wakiltar mai ɗakinsa.
Kotu ta Umarci a cigaba da tsare Sanata Ekweremadu da matarsa Hoto: thecableng Asali: UGC Manyan jiga-jigai a Najeriya sun halarci zaman Kotun na yau don sauraron shari’ar da ake wa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan.
Waɗan da suka halarci zaman sune; tsohonhttps://nigeria21.com/hau/https://nigeria21.com/hau/https://nigeria21.com/hau/ shugaban majalisa, David Mark, tsohon shugaban marasa rinjaye, Eyinnanya Abaribe, tsohon ƙaramin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, da kuma shugaban kwamitin harkokin waje na Sanatoci, Adamu Bulkachuwa.
Yadda zaman Kotun ya kasance Tun da farko, Luayan sanata ya musanta duk wata tuhumar amfana a Kes ɗin, “Mun musanta duk wani kalar amfana ko yunkurin hakan a gaba,” a cewar lauyan yayin da yake jawabin buɗe wa.
A zaman shari’ar lauyoyin da ke kare waɗan da ake ƙara sun yi musun cewa mutumin da abun ya shafa ƙaryar shekaru ya yi, yayin da masu ƙara suka tsaya kan bakarsu cewa yaro ne ƙarami.
Alkalin ya yanke cewa, wanda ake tafka muhawara kansa, David Okpo, kotu ba zata sake kallon shi a matsayin yaro ba, a cewar Kotun shekarun Okpo 21 ba 15 ba.
The Nation ta ruwaito cewa Sanata Ekweremadu da matarsa sun bayyyana a zaman yau Alhamis kuma sun musanta tuhumar da ake musu na yanke sassan jiki.
Kazalika an maida Kes ɗin Kotun manyan laifuka, kana aka umarci a cigaba da tsare waɗan da ake zargi har zuwa 4 ga watan Agusta.
A wani labarin kuma jirgin yaƙin NAF ya yi luguden wuta kan yan bindiga bayan kai wa Ayarin Buhari hari a Katsina Bayan harin da yan bindiga suka kai wa Ayarin shugaba Buhari, jirgin yaƙin NAF ya yi luguden wuta kan tawagar yan bindiga har biyu a Katsina.
Bayanai da suka biyo bayan samamen na sama sun nuna cewa jirgin ya hallaka aƙalla yan ta’adda 42 a kauyukan ƙaramar hukumar Safana.