Wata kotu ta Majistire da ke zamanta a Illorin ta jihar Kwara a ranar Laraba, ta umarci a ajiye mata babban likitan asibitin Ayodele Hospital, Ilorin a jihar Kwara, Dakta Ayodele Joseph, a gidan gyara hali bisa zargin da ake masa na yin fyade ma wata marar lafiya.
A cewar rahoton farko-farko na ‘yansanda (FIR), an zargi Joseph da yin fyade wa majinyaciyarsa wacce ta kasance ma’aikaciyar Nas ce da ta kwanta a asibitin domin jinyar rashin lafiyar da ya risketa.
Rahoton ‘yansandan ya yi nuni da cewa wanda ake zargin ya sanya wa majinyaciyarsa magani daga bisani ya mata fyade ba tare da amincewarta ba.
“A lokacin da Nas din ba ta da lafiya ta je asibitin domin neman jinya, yayin da ta nemi likitan ya duba lafiyarta, likitan da ya yi ikirarin ya na da kwarewar aiki na tsawon shekara 27 ya yi amfani da wannan damar.
“Bincike kan lamarin ya kai ga gano wani faifayin bidiyo da ke dauke da yadda fyaden ya wakana kuma gwajin da aka yi ya tabbatar da cewa an keta haddin Nas din har aka mata fyade,” a cewar FIR.
Mai gabatar da kara, Gbenga Ayeni, ya shaida wa kotun cewa duba da irin girman laifin da aka aikata ‘yansanda na neman kotun ta ajiye Ayodele a gidan yara.
A hukuncinsa, Magistrate Jumoke Kamson, ya amince da bukatar mai shigar da kara inda ya umarci a ajiye wanda Ake zargi a gidan gyara hali.
Daga bisani ya dage cigaba da sauraran karar zuwa ranar 18 ga watan Mayun 2023.