A wata sanarwa wacce babban lauya kuma wakilin tawagar lauyoyin Sheikh Ibrahim Zakzaky, Barrister Ishaq Adam ya fitar kuma aka yada kafafan sada zumunta na zaman ta bayyana kotu a babban birnin tarayyar Abuja ta soma zaman sauraron karar da lauyoyi suka gabatar dangane da takardun tafiyar babban Shehin malamin.
A zaman wanda aka gabatar jiya laraba an bayyana cewa lauyoyin wasu daga cikin wadanda ake kara basu samu halartar zaman ba amma tunda lauyoyin wasu daga cikin wadanda ake kara sun halarta kotu ta soma sauraron karar.
Sanarwar ta bayyana cewa, lauyan wanda ake kara na farko (DG IMMIGRATION) bai samu halarta ba, shima lauyan wanda ake kara na biyu (NIS) bai samu halarta ba.
Amma kotu batayi kasa a gwuiwa ba ta fara sauraron shari’ar a gaban lauyan wanda ake kara na uku (NIA) da kuma lauyan wanda ake kara na hudu DSS)
Duk wasu rantsuwa da lauyoyin wadanda ake kara suka shirya lauyoyin mai kara sun amsa, sa’annan kotu ta cigaba da zaman na sauraren karar.
A karshe kotu ta dage zaman zuwa ranar 30 ga watan maris domin yanke hukunci.
Sanarwar wacce Barista Ishaq Adam ya yadawa mutane tayi fatan nasara kuma tayi fatan samun nasarar gaskiya a kan zalunci.
A karshe tayi fatan kariya gami da lafiya ga Malam Zakzaky da mai dakin sa Malama Zeenah.
Shidai Malam Zakzaky yana karar wasu hukumomi bisa zargin rike masa takardun tafiya da akayi tattare da cewa yana son fita kasashen ketare domin neman lafiya.
Ratotanni sun tabbatar da cewa tun bayan sakin Jagoran na ‘yan uwa musulmi a Najeriyan daga kurkukun kaduna shi da mai dakin sa suke fama da rashin lafiya.
Sai dai da suka bukaci takardun su na tafiya (Passports) domin tafiya kasashen ketare neman magani kamar yadda kowa yake da ‘yancin yin hakan sai abu yaci tura sakamakon batan dabo da takardun tafiyar su sukayi.