Mai shari’a Chizoba Oji na babban kotu ta tarayya Abuja ta jingine umurnin da aka bada na kama shugaban EFCC na kasa, Abdulrasheed Bawa.
Hakan na zuwa ne bayan kotun ta ce ta gano cewa Bawa bai saba umurninta ba domin ya riga ya mayarwa wanda ya shigar da karar motarsa kafin yanke wancan hukuncin.
Kuma a halin yanzu wanda ya shigar da karar yana bin matakai a hukumar ta EFCC don ganin an biya shi kudinsa Naira miliyan 40 kamar yadda kotu ta umurta.
Babban kotun tarayya da ke Abuja ta jingine shari’ar da umurnin da aka bada na daure shugaban hukumar yaki da rashawa, EFCC, Abdulrasheed Bawa, kan saba umurnin kotu, rahoton Channels TV.
Mai shari’a Chizoba Oji ta jingine shari’ar a ranar Alhamis bayan sauraron wata bukatar da shugaban na EFCC ya gabatar.
An gabatar da bukatar ne bisa ga sashi na 6(6) (a) da sashi na 36(1) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 (wanda aka yi wa gyara), sashi na 91 na Sheriffs da Civil Process Act, Cap S6 Dokar Tarayyar Najeriya 2004 da sauran abubuwa masu alaka, Daily Post ta rahoto.
Kotun ta gano cewa a lokacin da aka bada umurnin, shugaban na EFCC bai saba umurnin kotu ba domin ya mayarwa wanda ya shigar da karar motar sa Range Rover da wasu abubuwa, mai shigar da karar kuma ya tuntubi hukumar ya fara bin hanyoyi tabbatar an biya shi kudinsa Naira miliyan 40 (40,000,000.00) Hukunci kan saba umurnin kotu.
Mai shari’a Chizoba Oji, a hukuncin da ta yi a ranar Talata, ta ce Bawa ya saba umurnin da kotu ta bayar da ranar 21 ga watan Nuwamban 2018, na mayarwa wanda ya shigar da kara motarsa Range Rover (super charge) da kudi Naira miliyan 40.
Ta kuma umurci a garkame Bawa a gidan gyaran hali na Kuje saboda saba umurnin kotu, da cigaba da yin hakan har sai ya wanke kansa.
Ta kuma umurci IGP na yan sanda ya tabbatar da hakan. Alkaliyar ta ki amincewa da uzurin da lauyan EFCC, Francis Jirbo ya bada don kare shugaban hukumar.
Tunda farko, kotun tarayya ta yanke hukuncin tura shugaban hukumar yaki da rashawa na EFCC, Abdulrasheed Bawa, gidan gyaran hali na Kuje kan saba umurnin kotu.
Kotun a ranar Talata, 8 ga watan Nuwamba, ta yanke wa Bawa hukunci, saboda saba umurnin kotu da ya danganci rashin aiwatar da umurnin kotu a baya.
Source:legithausang