Lamarin ya faru ne a lokacin shari’ar dan sandan nan farar fata mai suna Derek Chauvin, wanda ya kashe bakar fatar nan George Floyd, shi ma a Minneapolis a watan Mayun 2020, lamarin da ya haifar da zazzafar zanga-zanga a wancan lokacin.
Mutuwar Floyd ta janyo zanga-zangar adawa da wariyar launin fata da kuma cin zarafin da ‘yan sanda ke yi a fadin kasar.
Kotu dai ta yanke wa jami’ar ‘yar sandar hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari kan tuhuma ta farko da ake mata, yayin da tuhuma ta biyu kuma aka yanke mata shekaru goma.
Ko da yake jami’ar ta musanta zargin cewa da gangan ta yi harbin, tana mai nanata cewa hakan ya faru ne bisa kuskure.
A wani labarin na daban Miliyoyin al’umma a sassan duniya na shirin gudanar da bikin Kirismati a daidai lokacin da sabon nau’in cutar Korona na Omicron ke ci gaba da yaduwa, lamarin da ake ganin zai rage armashin bikin a bana.
Shekaru biyu kenan jere da juna da wannan annoba ta Korona ke haifar da cikas ga bikin na Kirismati.
A can Bethlehem kuwa, wurin da mabiya addinin Kitrista suka yi amanna cewa, nan ne mahaifar Annabi Isa Alaihi-s-salatu wassalam, masu gidajen otel-otel sun shiga damuwa saboda karancin baki da cutar ta Korona ta takaita adadinsu a bana, yayin da kuma Isra’ila ta rufe kan iyakokinta.
A tsakar daren yau Juma’a, wato jajibirin ranar bikin na Kirismatin, tsirarun mutane ne za su gudanar da taron addu’a a birnin na Bethlehem, al’amarin da ba a saba ganin haka ba.
Gwamnatocin kasashen Turai sun kafa wasu tsauraran ka’idojin yaki da cutar ta Korona, lamarin da ya rage wa bikin na Kiristamatio armashi.
Kasashe irinsu Netherlands da Spain da Italiya duk sun wajabta sanya takunkumin rufe baki da hanci musamman a bainar jama’a da zummar takaita yaduwar annobar a lokacin bikin na Kirismati.