Wata babbar kotu dake zama jihar Kano ta dage sauraron shari’ar ‘dan Chana da ya halaka budurwarsa ‘yar Najeriya.
Kamar yadda antoni janar na shari’a a jihar Kano ya bayyana, an aikewa ofishin jakadancin Chana da su aiko da tafinta domin Geng.
Kamar yadda lauya ya sanar, Geng Quangrong yana da hakkin fahimtar duk abinda ake tattaunawa a kotu yayin shari’ar.
Wata babbar kotu dake zama Kano mai lamba 17 dake zama a titin Miller karkasin jagorancin Mai shari’a Saunusi Ado Ma’aji ya dage sauraron shari’a Geng Quangrong, ‘dan kasar Chana da ake zargi da halaka budurwasa ‘yar Najeriya mai suna Ummukulsum Sani Buhari.
Wannan ya biyo bayan rashin tafinta wanda zai fassarawa ‘dan Chanann abinda ake fadi a gaban kotun, Daily Trust ta rahoto.
A zaman kotun da aka yi a yau, lauyan wanda ake kara, Muhammad Dan’azumi, ya mika bukatar cewa kotun ba za ta iya cigaba da zamanta ba saboda wanda ake zargin yana bukatar ya fahimci yaren da ake yi a gaban kotun.
A yayin jawabi jim kadan bayan zaman kotun, Antoni janar na jihar Kano kuma kwamishinan shari’a, M. A Lawan, yace an kasa sauraron shari’ar saboda wanda ake zargin yana da hakkin jin abinda ake tattaunawa da yaren da zai fahimta.
“An daga batun tafinta wanda batu ne na kundin tsarin mulki kuma bayan hukuncin karshe, mun aike da wasika ofishin jakadancin Chana inda muka bukaci tafinta saboda muna tsammanin hakan zai faru kuma na san zasu kawo.
“Hakan ne yasa muka dage sauraron shari’ar zuwa a kalla makonni uku. Ya dace a ce mako daya ne kadai.”
Daily Trust ta rahoto yadda kotun alkalin kotun Mai Shari’a Sanusi Ado Ma’aji ya dage shari’ar Geng Quangrong kan rashin lauya mai karesa a zaman karshe.
An dage sauraron shari’ar zuwa ranar 27 ga watan Oktoba. Wanda ake zargin da wacce ta mutun suna kasance masoyan juna kafin dangantakar ta lalace.
Dalilin Da Yasa Na Kashe Budurwata UmmuKulthum a Kano, Dan Chana Ya Magantu.
A wani labari na daban, mutumin nan ɗan China mazaunin jihar Kano, Geng Quangrong, ya bayyana cewa ya soka wa budurwarsa, Ummu Kulthum, wuƙa har lahira ne saboda ta ci amanarsa.
Idan baku manta ba, ɗan China ya je har gidansu budurwar dake Anguwar Kabuga, Ɗorayi Babba, ya kasheta ranar Jumu’a da ta gabata, kamar yadda PM News ta ruwaito.
Deng ya amsa laifinsa na aikata kisan kai bayan dakarun ‘yan sanda sun kama shi a jihar Kano.
Source:legithausang