Kotun Majistire mai lamba ta daya da ke Bauchi ta amince da bukatar bayar da belin Dakta Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi bisa sharadin guda uku.
Idan za a tuna dai, ‘yansandan sun gurfanar da Malamin ne a gaban kotun bisa zarginsa da tada zaune tsaye da ka iya barazana ga zaman lafiyan jama’a. Kuma hakan ya biyo bayan korafin da kungiyar Fitiyanul Islam ta shigar ne a kansa.
Da ya ke yanke hukunci kan bukatar belin, Mai Shari’a Abdulfata Baba Shakoni, ya ce, ya amince da bukatar belin malamin bisa sharadi guda uku, na farko zai kawo Hakimi, na biyu Babban Sakatare da ke aiki a karkashin Gwamnatin jihar Bauchi da kuma wani Malami da ke kwayan Bauchi.
Kazalika, ofishin Antoni Janar kuma kwamishinan shari’a ta jihar Bauchi sun bukaci kotun da ta amince musu su amshi ragamar karar daga hannun ‘yansanda domin cigaba da Shari’ar.
Daga bisani kotun ta amince da wannan bukatar.
Da ya ke karin haske kan hukuncin, daya daga cikin lauyoyin da suke kare malamin, Barista Sadik Abubakar Ilelah, ya nuna farin cikinsu bisa samun belin malamin tare da cewa insha Allahu za su cika sharudan da Alkalin ya gindaya.
Da yake bayani kan amsar ragamar karar da suka yi, daya daga cikin lauyoyin a ma’aikatar shari’a ta jihar Bauchi, Aliyu Ibn Idris, ya ce, “Shi Antoni Janar na jiya ko na tarayya yana da dama da dalili ba dalili ya shiga cikin kara.”
“Antoni Janar ya shigo ya karbi Kes ba sabon abu ba ne. Iyakaci abun da za a duba shigowar tamu za ta haifar da adalci ko ba za ta haifar da adalci ba. Insha Allahu za mu yi iyaka abun da za mu yi a wanzan da adalci a kai,” Inji shi.
Sannan, ma’aikatan shari’an ta bukaci ‘yanda da su ba su kundin Shari’ar da sauran abubuwan da suka hada wajen shigar da cajin domin nazarin akwai bukatar canzawa ko a’a.Daga bisani dai Alkalin ya dage shari’ar zuwa ranar 24 ga watan nan da muke ciki domin cigaba da shari’a.
Wakilinmu ya labarto cewa an sake komawa da malamin zuwa gidan yari har zuwa lokacin da za su cika sharadin belin.