Kotu ta amince da korar ƴar sandan Najeriya da ta ɗauki ciki ba ta da aure.
Wata babbar kotun tarayya a Najeriya ta amince da matakin da rundunar ƴan sandan ƙasar ta ɗauka na korar wata jami’ar da ta ɗauki ciki a shekarar da ta gabata.
Mai shari’a Inyang Ekwo ya ce bai ga wani ƙwaƙƙwaran dalili ba na “haifar da ruɗani ga tsarin rundunar ba”.
Ya ƙara da cewa “Duk wanda da ya shiga rundunar dole ne ya kiyaye dokokinta ko kuma kada ya shiga rundunar saboda babu tilas game da zama mambanta.”
Ƙungiyar lauyoyin Najeriya ce ta shigar da ƙarar bayan korar wata jami’ar ƴan sanda ta yi ciki ba ta da aure a watan Janairun 2021.