Kotu a Lardin Arewacin Illinois da ke kasar Amurka, ta umarci jami’ar jihar Chicago (CSU) da ta saki bayanan karatun shugaban kasar Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ba tare da bata wani lokaci ba.
Hakan na zuwa ne bayan da kotu ta ki amincewa da daukaka karar da Tinubu ya yi da ke neman a hana aiwatar da hukuncin da karamar kotu ta yanke na cewa a fitar da bayanan.
Wannan matakin na zuwa ne bayan da wata mai shari’a a Amurka, Nancy Maldonado, ta amince da hukuncin da Alkalin Kotun Majistire Jeffrey Gilbert na kotun lardin US da ta bada umarni ga CSU da ta gaggauta fitar da bayanan karatun Tinubu.
Tinubu dai ya kalubalanci hukuncin na kotun majistire din ne ta bada umarni a saki bayanan karatunsa.
A cewar Tinubu, fitar da bayanan karatunsa zai haifar masa da babbar illa kuma tona sirrinsa ne kuma fitar da bayanan karatun bai da wata alaka kan karar da ake yi akansa na tuhumar nasarar lashe zabensa.
Atiku dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, wanda suka fafata neman kujerar shugaban kasa tare da Tinubu a ranar 25 ga Fabrairun 2023, ya nemi a saki bayanan karatun Tinubu domin ya na zargin cewa, Tinubu ya gabatar da shaidar karatu na bogi ga hukumar zabe ta kasa (INEC).
Kotun ta bai wa jami’ar wa’adin wa’adin zuwa ranar Litinin da ta shirya bayanan karatun Tinubu sannan a mika bayanan kafin zuwa ranar Talata da karfe 5 na yamma.
Amma mai shari’ar ta ce, Tinubu yana da damar daukaka kara kai tsaye zuwa kotu ta gaba (Seven Circuit).
Source: LEADERSHIPHAUSA