Wata Kotu a Abuja dake Najeriya ta tabbatar da shugabancin Alhaji Ahmadu Danzago a matsayin shugaban Jam’iyyar APC dake Jihar Kano saboda yadda ta gudanar da tarurrukan Jam’iyyar a matakan mazabu da kananan hukumomi da kuma Jiha.
Alkalin kotun yayi watsi da bukatar bangaren Gwamna Ganduje na dakatar da shari’ar, yayin da ya umurce su da su biya tarar naira miliyan guda saboda abinda ya kira bata lokacin kotu.
Kotu ta amince da tarurrukan da bangaren Malam Shekarau ya gudanar wanda ya tabbatar musu da shugabancin Jam’iyyar a Jihar Kano.
Jam’iyyar APC a Jihar Kano ta fada rikicin cikin gida a tsakanin ‘yayan ta lokacin gudanar da tarurrukan zaben shugabanni a matakai daban daban, abinda ya kaiga samun bangarori guda biyu da suka hada da na tsohon Gwamna Malam Ibrahim Shekarau da kuma na Gwamna mai ci Abdullahi Umar Ganduje.
Wannan ya kaiga gudanar da tarurrukan jam‘iyyar guda biyu da kuma samun shugabannin bibbiyu a matakai daban daban na jihar.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewar ‘Dan Majalisar Tarayya dake wakiltar Jihar Kano Sha’aban Sharada ya dauki nauyin shari’ar da kuma tarurrukan bangaren jam’iyyar dake kalubalantar Gwamna Ganguje.
A bangare guda Gwamna Abdullahi Ganduje ya bukaci ‘yayan jam’iyyar APC a Jiahr da su kwantar da hankalin su dangane da wannan hukunci, inda yace suna ci gaba da nazari akan sa.
Wata sanarwa da kwamishinan yada labaran jihar Mohammed Garba ya rabawa manema labarai yace tunda rikici ne na cikin gida, gwamnati da APC na nazari domin dubar mataki na gaba da za’a dauka.
Gwamnan ya kuma bukaci jami’an tsaro da su tashi tsaye domin tabbatar da doka da oda dangane da masu fakewa da hukunci domin aikata laifuffuka.
Masu sharhi na kallon wannan mataki a matsayin babbar kalubale ga jam’iyyar wadda ke shirin tinkarar zabe mai zuwa da kuma rarrabuwar kawunan da ake samu.
Jihar Kano na da matukar tasiri ga siyasar Najeriya da kuma ita kan ta Jam’iyyar APC.
Irin wadannan rikice rikice da Jam’iyyar APC ke fuskanta ya sanya ta jinkirta taron ta na kasa domin zaben shugabanni zuwa shekara mai zuwa.