Koriya Ta Arewa Ta Harba Wani Makami Da Bai Yi Nasara Ba.
Rahotanni daga yankin Koriya na cewa, koriya ta Arewa ta harba wani makamai wanda bisa ga dukkan alamu bai yi nasara ba.
Wata sanarwa da rundinar sojin Koriya ta kudu ta fitar ta ce, makobciyarta ta harba wani makami da ba’a tantance ba a wani yanki na Sunan a safiyar yau da misalin karfe 9:30 agogon wurin, saidai a cewarta makamin ya cutura jin kadan bayan harba shi.
Bayanai sun ce wannan gwajin da ya yi nasara shi ne irinsa na goma da Pyongyang, zata yi tun farkon wannan shekara.
Koriya ta Arewa ta yi nasarar harba makamai masu linzami guda bakwai da kuma wasu guda biyu da ta ce taurarun dan adam ne na bincike.
READ MORE : Da alama tsohon ministan Isra’ila ya kai wa Iran hari a Erbi.
Koriya ta kudu da kuma Amurka sun bayyana cewa gwajin da koriya ta Arewa ta yi a makon da ya gabata na wani sabon makamai mai linzami ne dake kaiwa daga wannan nahiya zuwa waccen, kuma masana harkar tsaro sun danganta makamin da shu’umi da ba’a taba yin irinsa ba a cen baya.
READ MORE : An duba lafiyar Sarkin Saudiya.