Za ayi shari’a nan gaba a kotu tsakanin Gwamnatin jihar Kogi da kamfanin Dangote Industries Ltd.
Dangote Industries Limited ne suke da kamfanin Dangote Cement Plc da aka samu sabani da su a jihar Kogi.
Gwamnatin Kogi tana so kotu ta duna yarjejeniyar da aka shiga da Dangote tun a shekarun 2002 da 2003.
Gwamnatin jihar Kogi ta shigar da kara a kan kamfanin Dangote Industries Limited wanda ya mallaki kamfanin siminti na Dangote Cement Plc.
This Day tace gwamnatin Kogi ta shigar da kara a dalilin sabanin da aka samu game da mallakar kamfanin siminti na Obajana da yake Oworo a jihar Kogi.
Kamar yadda takardar karar mai lamba HcL/8T/2022 ta nuna, za ayi a shari’a tsakanin Gwamnati da kamfanin a babban kotun jiha da ke Lokoja.
A ranar 18 ga watan Oktoban 2022, gwamnatin Kogi ta shigar da kara a gaban Alkali, tana mai neman a raba gardamar da ke tsakaninta da kamfanin.
An dauko maganar shekaru 20 An nemi kotu ta duba yarjejeniyar da aka yi takanin Gwamnatin Kogi da Dangote Industries Limited a karshen Yulin 2002 da kuma Fubrairun 2003.
Lauyoyin gwamnati sun ce ba a bi ka’ida wajen shiga yarjejeniya shekaru 20 da suka wuce ba.
Punch ta kara da cewa idan har hakan ta tabbata, gwamnatin ta roki Alkali ya soke yarjejeniyar da ke tsakanin bangarorin domin an rasa ginshiki.
Bugu da kari, gwamnatin jihar tana ikirarin kamfanin na Dangote ba zai iya cin moriyar wata dama, riba ko amfani daga yarjejeniyar nan da aka yi ba.
Har ila yau, gwamnatin Kogi tana so kotu ta takawa Dangote Industries Limited burki, ta hana kamfanin amfana da yarjejeniyar da aka sa wa hannu.
A Wata Jahar Arewa Ba a sa ranar zama ba tukuna Jaridar ta nemi jin ta bakin sashen rajistar kamfani da Dangote, amma ba ayi nasarar samun su ba.
Har zuwa yanzu ba a sa lokacin da za a saurari shari’ar ba.
A cikin takardun da aka bada domin gamsar da kotu, akwai bayanin SSG, Folashade Arike Ayoade da tace jihar Kogi tayi wa kamfanin Obajana rajista a 1992.
Yadda muka mallaki Obajana:
DIL Kwanaki kun samu labari cewa wani jawabi da aka fitar ya yi karin haske a kan sabanin da ya shiga tsakanin Dangote da kuma gwamnatin jihar Kogi.
Shugabannin kamfanin Dangote Industries Ltd sun ce sun biya kudi wajen sayen kamfanin Obajana a 2002, kuma gwamnatin tarayya ta ba su lasisi.
Source:legithausang