Ko kun san abubuwan da ke lalata ƙuri’unku a lukutan zaɓe?
Babu wanda zai ji daɗi ya ga ya sha wahala wurin yin katin zaɓe da bin layin karɓar katin idan ya fito, a ranar zaɓe ya kaɗa kuri’arsa ace ta lalace ba a ƙirga da ita ba.
Yau she ne kuri’ar mutum ke lalacewa? Tayaya za a iya kauce wa faɗawa irin wannan yanayi? sannan ta wacce hanya mutum zai kauce wa ƙin tantancewar na’ura a lokutan zaɓe?
Wata maƙala da BBC ta himmatu wajen rubutawa ke nan domin taimaka wa masu zaɓe musamman matasan da za su fara zaɓe a wannan karon.
BBC ta tattauna da mai magana da jami’ar hukumar INEC, Zainab Aminu Abubakar domin jin amsar tambayoyin nan da muka jero.
Zainab Aminu ta ce cikin manyan abubuwan da ke ɓata ƙuri’ar mai kaɗa ta shi ne gaza dangwala ɗan yatsa a daidai gidan da aka ware domin jam’iyyar da yake son zaɓe.
Wannan hoton na sama ya nuna ɓangare biyu na takardar kaɗa kuri’a, wadda aka yi daidai da wacce aka yi ba daidai ba.
Wadda ke ɓangaren hannun hagun mai karatu ita ce aka kaɗa a daidai saboda zanen hannun ya shiga cikin zanen jam’iyyar da yake so kamar yadda INEC ta umurci kowa ya yi.
Wadda ke ɓangaren dama kuwa babu ko ɗaya da aka kaɗa daidai saboda ta fita daga gidan da aka ware domin mai ƙada ƙuri’ar ya zaɓi jam’iyyar da yake so.
Abin da ya sa ake guje wa hakan shi ne, kada a samu rikici wajen ƙirga kuri’un saboda idan ta taɓa gidan sama, mai jam’iyyar zai iya cewa shi aka dangwala mawa, kazalika wanda yake a ƙasa ma zai iya wannan iƙirarin.
Babu buƙatar tawwadar zaɓe ta yi yawa a hannu
Wata matsalar ita ce yadda masu kaɗa kuri’a suke dagwalo tawwadar da ake dannawa a jikin takardar zaɓe, ruwa ne da yake da saurin bushewa amma kuma yana naso ta yadda idan aka manna shi da jikin takardar zai iya shiga wani gidan da ba a yi niyya ba.
“Rashin natsuwa ne sau da dama yake jefa mutane cikin irin wannan yanayi da har zai kai ga lalacewa ƙuri’ar, saboda duk wadda ta yi naso zuwa wani gidan ba a ƙirga ta cikin masu kyau,” in ji Hajiya Zainab.
Lalle kan iya bayar da matsala a da, ba a yanzu ba
A baya da ake da hanya ɗaya tal ta tantance mai kada ƙuri’a, da na’urar da ke tantance ɗan yatsa, an yi ta fama da matan da ke yin lalle saboda na’urar ba ta fiye tantance zanen hannunsu ba.
“Na’urar da aka kawo za a yi aiki da ita yanzu tana da zaɓi biyu, za ta iya tantance zanen ɗan yatsan mutum ko kuma tantance fuskarsa.
“Ko da zanen hannu bai ɗauka ba saboda wasu dalilai irin na su lalle, babu damuwa saboda babu wannan barazanar kwata-kwata,” in ji Hajiya Zainab.
Matsalar ƙaruwa take yi
Alƙaluman hukumar zaɓe mai zamankanta sun nuna cewa an samu ƙuri’un da suka lalace kimanin miliyan ɗaya da dubu ɗari biyu da tamanin da tara a 2019.
Hakan na nufin an samu ƙaruwar ƙuri’un da suka lalace 445,000 a shekarar 2019 idan aka kwatanta da waɗanda aka samu a 2015.
Hakan dai koma baya ne a wajen hukumar da kuma masu zaɓe baki ɗaya.
“Burin INEC a yi zaɓe lafiya a gama lafiya ba tare da rikici ba da kuma lalacewar ƙuri’u masu yawa ba.
“Kawai dai za mu ci gaba da faɗakarwa har mutane su gane a baya mun yi kuma muna kan yi har yanzu,” in Zainab ta INEC.