Jaridar Tribune a labaran ta na ranar asabar ta rawaito cewa, wani lauya mazaunin Abuja, Bala Dakum ya shigar da Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-rufa’i kara a babbar kotun duniya wacce aka fi sani da ICC, yana mai rokon kotun tayi bincike gami da hukunta el-rufa’i a kan kisan ‘yan Shi’a a jihar ta Kaduna.
Da yake tattaunawa da ‘yan jarida a Abuja Dakum ya bayyana cewa, har an rubuta karar a lokacin da yake maganar.
Lauyan ya kuma bukaci kotun ta ICC da ta binciki kuma ta hukunta tsohon babban hafsan sojin Najeriya, General Tukur Burutai (rtd) da kuma kwamishinonin ‘yan sanda wadanda sukayi aiki a shekarar 2015 lokacin gwamna El-rufai ya karbi ofishin gwamnan jihar.
Kamar yadda Tribune ta rawaito Dakum ya bayyana cewa, tun lokacin da El-rufai ya karbi iko a jihar Kaduna a shekarra 2015 ya shiga sabgogin kisa gami da laifuka a kan wadanda yake wakilta watau ‘yan uwa musulmi ‘yan shi’a a Kaduna.
Lauyan ya kara da cewa, dalilin wannan kara wacce aka shigar wannan satin shine, domin a gayyaci kotun ICC ta gudanar da bincike kuma a hukunta laifuka gami da kisan da Mallam Naisir Elrufa-i ya gudanar a kan wadanda yake wakilta, watau ‘yan shi’a.
A cigaban bayanin sa Dakum ya kuma bayyana cewa, Buratai da sauran kwamishinonin da sukayi aiki a shekaru 8 na mulkin El-rufai sun taimaka sosai wajen aiwatar da wadannan laifukan da ake magana a kai.
Lauyan ya bayyanan cewa, wadanda yake wakilta suna da fatan kotun ICC wacce ke karkashin Dokar Roma “Rome Statue” domin tayi bincike kuma ta hukunta wadanda suka aikata laifi gamin da kashe kashe da kuma sabawa dan adamtaka zatayi aiki da sauri.
Lauyan ya bayyana cewa, wannan kira yana zuwa ne a karshen mulkin Gwamna Mallam Nasir El-rufai domin bazai kuma samun kariyar ofishi ba.
Lauyan ya kuma kirayi sabuwar gwamnati da kada ta bawa Mallam Nasir El-rufai kowanne mukami kamar yadda gwamnatin Shugaba Buhari ta bawa Burutai mukamin ambassada domin kada a siffanta kasar a mummunan yanayi.