An fara zaman makokin kwana uku a Jamhuriyar Nijar daga Talatar nan, bayan kisan sojojin kasar 29 a wani harin da ake kyautata zaton ‘masu ikirarin jihadi ne suka kai.
Shi ne hari mafi muni tun bayan da sojojin suka kwace mulki a watan Yuli.
Tashin hankalin na baya-bayan nan ya zo ne a daidai lokacin da masu juyin mulkin Nijar suka nuna cewa suna nazarin tayin da makwabciyarsu Aljeriya ta yi na shiga tsakani a tattaunawar mika mulki ga farar hula.
Nijar na fama da tashe-tashen hankula biyu na ‘yan ta-da-kayar-baya da suka hada da wanda ya mamaye sashen Kudu maso Gabashin kasar daga yakin da aka dade ana fama da shi a Nijeriya mai makwabtaka, da kuma hare-haren masu ikirarin Jihadi da ke tsallakawa daga Mali da Burkina Faso.
A lokacin da shugabannin sojojin suka hambarar da zababben shugaban kasar Mohammed Bazoum ranar 26 ga watan Yuli, sun kafa hujjar yin hakan a kan tabarbarewar harkokin tsaro.
An kai harin ne na ranar Litinin a Yammacin Nijar da “bama-bamai da motocin kai hare-haren kunar bakin wake da ‘yan mayaka fiye da dari suka kai”, in ji ma’aikatar tsaro cikin wata sanarwa da aka watsa ta gidan talbijin.
Ma’aikatar tsaron ta kara da cewa sojoji biyu sun samu munanan raunuka sannan kuma anyi kisan ‘yan ta-da-kayar-baya masu yawa.
Harin dai ya faru ne a arewa maso Yammacin Tabatol, kusa da kan iyakar kasar Mali, wadda ke fama da rikicin mayaka masu alaka da kungiyar IS da kuma Al-Kaeda.
Tashe-tashen hankula a yankin mai lakabin “iyaka uku” da ke tsakanin Nijar da Mali da kuma Burkina Faso, ya haddasa juyin mlukin soji a dukkan kasashen uku tun daga shekara ta 2021.
Source LEADERSHIPHAUSA