Kungiyar kiristoci na CAN na reshen Arewacin Najeriya sun barranta daga goyon bayan APC.
Sakataren CAN, Sunday Oibe ya bayyana cewa ba su tare da Bola Tinubu/Kashim Shettima a 2023 Oibe ya yi kira ga shugaban kasa da ‘Yan siyasa, sannan ya taya sabon shugaban CAN murna.
Kungiyar kiristoci a Najeriya watau CAN na reshen Arewacin Najeriya ta tabbatar da cewa ba su goyon bayan APC a zaben shugaban kasa.
Sakataren kungiyar ta CAN, Sunday Oibe ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar a karshen makon da ya gabata, Channels TV ta kawo wannan labari.
Sunday Oibe ya jaddada matsayar kungiyar Kiristan saboda matsayar da jam’iyyar APC ta dauka na tsaida Musulmi da Musulmi a zaben shugaban kasa.
“Mu na tabbatar da matsayinmu a kan batun tikitin Musulmi da Musulmi a kasa mai tarin kabilu da addinai irin Najeriya.
Musamman idan aka yi la’akari da cewa ba a taba samun lokacin da aka raba kai ta fuskar addini da kabilanci irin haka ba.”
Sakataren kungiyar yace CAN ba za ta zauna da wani ‘dan siyasa ko jam’iyyar siyasa a boye ba. Matsalar tsaro a yau.
Amma duk da haka, shugaban kiristocin yace za su bar kofa a bude ga duk wani mai sha’awar zama da su domin kawo shawarar yadda za a gyara Najeriya.
A jawabin na sa, Oibe ya yi tir da yadda tsaro ya tabarbare, ya yi kira na musamman ga shugaba Muhammadu Buhari ya tashi-tsaye wajen kare mutanensa.
“’Yan ta’adda sun yi wa Najeriya zobe, suna tafka ta’adi a kan al’umma, suna gurgunta tattalin arziki da rayuwar mutanen kasa.
Musamman a jihohi kamarsu; Kaduna, Katsina, Zamfara, Niger, Benue, Plateau, Taraba, Kebbi, Sokoto, da Abuja – birnin tarayya. – Sunday Oibe.
Mubaya’a ga sabon shugaban CAN Kamar yadda jaridar nan ta Punch ta kawo rahoto, CAN ta yi kira ga shugaban kasa da majalisar tarayya suyi maza su dauki matakan da suka dace.
A karshe, a madadin daukacin Kiristocin da ke jihohi 19 na Arewa da birnin Abuja, Oibe ya taya Rabaren Daniel Oko murnar zama shugaban CAN.
An tasa Dogara, Babachir gaba Mun samu rahoto cewa rikicin da ake yi a jam’iyyar APC a game da tikitin Musulmi da Musulmi da aka yi a zaben 2023 ya jawo ana wasan tonon silili.
Ana zargin Babachir Lawal da Yakubu Dogara sun yi wa Bola Tinubu aiki ne a APC, suka hana Yemi Osinbajo samun takara, sai yanzu suke yin nadama.
Source:hausalegitng