Kirista daga kudu ne ya kamata ya gaji Buhari_Inji CAN.
Kungiyar Kiristocin Najeriya da aka fi sani da CAN ta bayyana cewa, Kirista daga kudu ne ya kamata ya gaji shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Shugaban kungiyar, Rev Samson Ayokunle ne ya bayyana haka yayin karbar tawagar turawa masu saka ido kan harkar zabe.
Yace matsalar tsaron da akw fama da ita ba lallaine a samu yin zaben gaskiya ba.
Yace CAN bata da zabin wanda take son ya zama shugaban kasa amma ya kamata ace Kirista ne.