Kimanin Yara Miliyan 18.5 Ne Ba sa Zuwa Makaranta A Najeriya Inji UNICEF.
Kididdigar baya-bayan nan da hukumar kula da Ilimi da yara kanan ta Majalisar dinkin duniya UNICEF ta fitar ya nuna cewa adadin wadanda ba sa zuwa makaranta a nigeriya ya karu sosai idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata ta 2001, wato miliyan 10.5.
Shugabar ofishin hukumar ta UNICEF a jihar Kano Rahma Farah ta shaidawa maneman labara cewa A halin yanzu a Najeriya kimanin kashi 60% na yara basa zuwa makaranta inda sama da miliyan 10 daga cikin yara mata ne,
Hare-haren da kungiyoyin masu ikirarin jihadi day an ta’adda ke kaiwa a Arewacin Najeriya ya cutar da ilimin yara a kasar, kuma ya samar da mummunan yanayi da hakan ya kashe karfin guiwar iyaya da masu ruwa da tsaki wajen aikewa da Yayansu makarantu,
Batun yin auren wuri da daukar ciki da wuri sun sa matsalar ta kara kamari.
READ MORE : Iran; Za’a Iya Kulla Yarjejeniya Idan America Ta Dawo Cikin Jarjejeniyar Da Aka Cimma.
Rikece-rikece da yin garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa sun tilastawa mahukumta rufe makarantu fiye da 11000 a fadin kasar a watan Disemba a shekara ta 2020 kamar yadda hukumar ta Unicef ta bayyana.