Gwamnatin kasar Kenya ta bada sanarwan cewa ta kusan kammala tattaunawa da gwamnatin kasar Qatar don ganin irin tallafin da zata bawa kasar a bangaren tabbatar harkokin tsaro a gasar kwallon kafa ta FIFA 2022 wanda za’a gudanar a karshen shekara mai zuwa a birnin Doha.
Jaridar The Nation’ ta kasar Kenya ta nakalto ministan harkokin cikin gida na kasar Kenya Dr. Fred Matiang’i, yana cewa har yanzun suna cikin tattaunawa da Sheikh Khalid bin Khalifa bin Abdulaziz al-Thani firai ministan kasar Qatar kan wannan batun.
Dr Matiang’i ya bayyana haka ne a ofishin jakadancin kasar Qatar a birnin Nairabo, a lokacinda ya halarci bikin ranar samun ‘yencin kan kasar Qatar, bisa gayyatar jakadan kasar Qatar a Kenya, wato Jabor bin Ali al-Dosari .
Labarin ya kara da cewa za’a gudanar gasar wasannin kwallon kafa ta FIFA 2022 A filayen wasannin guda 8 a birnin Doha babban birnin kasar ta Qatar, daga ranaku 21 ga watan Nuwamba zuwa 18 ga watan Dicemba na shekara ta 2022.
Har’ila yau kasashen biyu suna tattauna dangane da samar da cibiyar bada Visar hallatar na FIFA 2022 a birnin Nairobi babban birnin kasar ta Kenya, inji Dr Matiang’i. Har’ila yau akwai batun daukar karin ma’aikata wadanda zasu gudanar da harkokin khidima a wasan daga kasar Kenya. Kasar Qatar tana bukatar ma’aikata kimani 37,000 don yin khidimomi daban-daban a lokacin gasar wasannin na FIFA 2022.