Kenya Jami’an Tsaro Na Cikin Shirin Ko Ta Kwana Saboda Barazanar Tsaro
Kasar Kenya ta tsaurara matakan tsaro a babban birnin kasar, Nairobi da wasu biranen kasar bayan da wasu kasashen Turai suka yi gargadin yiwuwar kai hare-hare.
An ga jami’an ‘yan sanda dauke da manyan makamai na ta sintiri a titunan birnin Nairobi ranar Juma’a, yayin da aka tsaurara tsaro a ofisoshin gwamnati da gine-ginen jama’a da kuma manyan kantuna.
Ofishin jakadancin Faransa a Kenya ya fitar da wata sanarwa inda acinta ya gargadi ‘yan kasarsa kan “hadarin kai hari a Nairobi cikin kwanaki masu zuwa” a yana mai ba da shawarar “kaurace wa wuraren da ‘yan kasashen waje ke zuwa” kamar otal-otal, gidajen cin abinci da manyan shaguna.