Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya bukaci a tura masa Bataliyar soji a jihar domin kwato wuraren da ‘yan ta’adda ke yadda suke so a wasu yankunan jihar.
Ya yi wannan rokon ne a ziyarar da ya kai wa babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, a hedikwatar sojoji da ke Abuja.
Gwamnan ya yi alkawarin samar da duk abinda ake bukata don karbar bataliyar a jiharsa.
LEADERSHIP ta rahoto cewa, Bataliya – tana dauke da dakarun soji 300 zuwa 1,000.
A nasa jawabin, babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya yi alkawarin tura karin dakarun soji zuwa jihar Taraba.
Sai dai ya yi nuni da cewa, akwai wata bataliya a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan a jihar Borno, amma dai ya yi alkawarin samar da karin wata tawagar gaggawa ta sojin zuwa jihar Taraba.
A jiya da dare,aka samu harin bindiga a jami’ar Morgan da ke jihar Maryland ta kasar Amurka, harin da ya jikkata wasu mutane biyar.
Hakika, hare-haren bindiga na kara addabar yara da matasa a kasar Amurka. Alkaluman da cibiyar rigakafi da shawo kan cututtuka ta kasar Amurka ta samar a kwanan baya sun yi nuni da cewa, hare-haren bindiga sun zarce hadurran mota har sun zo na farko a matsayin dalilin mutuwar yara da matasa a kasar.
An Yabawa Ci Gaban Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin Yayin Liyafar Da Aka Shirya Domin Murnar Cikarta Shekaru 74 Da Kafuwa
Han Zheng Ya Yi Kira Ga Sin Da Amurka Da Su Kyautata Matakan Shawo Kan Sabani
Alkaluman sun shaida cewa, daga shekarar 2019 zuwa ta 2021, yara da matasan da suka halaka sakamakon hare-haren bindiga sun karu da kaso 50%, ko a shekarar 2021 kadai, kimanin kaso 19% na mutuwar yara da matasa na da alaka da hare-haren bindiga.
Lamarin da ya sa na tuna da wani hoton bidiyon da aka watsa ta yanar gizo a bara, wanda ya janyo cece-kuce daga masu kallonsa.
Bidiyon ya nuna yadda wata ‘yar Amurka ta sayo wa danta mai shekaru 5 da haihuwa wata jakar karatu da za ta iya kare shi daga harbin bindiga, tare da horar da shi a gida kan yadda zai iya gudu daga hare-haren bindiga. Wadanda suka kalli bidiyon da dama sun ce, hakan abin bakin ciki ne.
Babu shakka, sai dai gaskiyar lamarin da ya faru ya fi hakan bakanta wa mutane rai, alkaluman da cibiyar kididdigar harkokin ba da ilmi ta kasar Amurka(NCES) ta samar sun yi nuni da cewa, daga shekarar 2021 zuwa ta 2022, gaba daya an samu lamuran harbe-harben bindiga 327 a makarantun kasar, ciki har da na firamare da na sakandare, kuma 188 daga cikinsu sun haifar da mutuwar mutane ko jikkatarsu.
Source: LEADERSHIPHAUSA