Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba, a ranar Laraba, ya ba da umarnin rufe makarantar sakandaren kimiyya ta gwamnati da ke Jalingo cikin gaggawa sabida tabarbarewar gine-ginen makarantun.
Kefas wanda ya kai ziyarar bazata makarantar da misalin karfe 12:00 na rana, ya kadu matuka game da halin da daliban suke ciki – mummunan halin da azuzun karatu da dakunan kwanan daliban ke ciki.
Gwamnan wanda ya samu rakiyar sakataren gwamnatin jihar, Cif Gibon Kataps; kakakin majalisar dokokin jihar Taraba, Kizito Bonzina, da sauran jami’an gwamnati, ya nuna takaicinsa kan lamarin, ya kuma yi alkawarin gyara makarantar zuwa tsalelen ginin zamani.
Ya kuma ba da umarnin rufe makarantar cikin gaggawa domin gwamnatin ta samu damar fara aikin gyare-gyaren don inganta jin dadin daliban da malamansu.
A wani labarin na daban kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta kammala daukar matashin dan wasan tsakiya daga Borrusia Dortmund akan zunuzurutun kudi Yuro miliyan 103
Bellingham wanda ya je Dortmund shekaru uku da suka gabata ya godewa Magoya bayan tsohuwar kungiyar tasa inda yace duk da yana fatan nasara a sabuwar kungiyarsa amma ba zai taba mantawa da kungiyar ta Jamus ba
Real Madrid na neman karfafa yan wasansu bayan tashin da wasu Yan Wasa sukayi da Suka hada da Benzema,Hazard,Asensio da kuma Mariano Diaz
Bellingham wanda ya lashe kyautar gwarzon Dan wasan gasar Bundesliga ta kasar Jamus ya zama Dan wasa na biyu mafi tsada da Real Madrid ta taba saye bayan tsohon kyaftin din tawagar kwallon kafa ta Belgium Eden Hazard