Hidayet Bayraktar ya yi albishir da cewa kayan yakin da Najeriya take sauraro daga Turkiyya za su iso.
Jakadan na Turkiyya a Najeriya yace wannan yana cikin yarjejeniyar da aka yi alkawari a shekarar 2021.
Kayan da za a aiko za su taimaka a yakar matsalar rashin tsaro da kuma fatattakar kungiyoyin ta’adda.
Jakadan kasar Turkiyya a Najeriya, Hidayet Bayraktar yace kayan aikin da aka saya domin magance matsalar tsaro su na daf da karasowa.
Daily Trust tace Hidayet Bayraktar ya yi wannan bayani a wajen bikin da kasar take yi a Abuja.
Jakadan kasar ya shaidawa jama’a cewa Turkiyya za ta ba Najeriya jirage marasa matuki da jirgi masu sukar ungulu kamar yadda aka yi alkawari.
Hidayet Bayraktar yace gudumuwar da kasarsa za ta ba Najeriya yana cikin nasarorin da aka samu a yarjejeniyar hadin-kan da aka shiga a 2021.
Za mu taimakawa Najeriya
Turkiyya An rahoto Jakadan yana mai cewa a shirye kasar Turkiya take wajen ganin ta taimakawa Najeriya ta yaki matsalar tsaro da fasahohin zamani.
“Yarjejeniyar tsaron da kasashenmu suka shiga a shekarar bara ya bude sabon shafi.
Bisa wannan dama, ina mai alfaharin bada sanarwar cewa wasu daga cikin kamfanonin tsaronmu Bayraktar (TB-2) da (T-149) ATAK za su zo Najeriya.
Bayraktar (TB-2) kamfani ne da yake kera jirage marasa matuki yayin da kamfanin (T-149) ATAK ya kware wajen aikin kera jirage masu saukar ungulu.
Kamar yadda The Cable ta kawo rahoto, kayan aikin za su taimakawa gwamnati da mutanen Najeriya wajen inganta tsaro da ganin an kawo zaman lafiya.
Alakar kasashen 2 tana kara kyau
Har ila yau, Jakadan kasar yace yana sa ran gwamnatin Najeriya ta maida alheri ta hanyar yakar duk kungiyoyin ta’adda na FETO da ke zama a kasar nan.
Ministan harkokin kasar waje, Amb. Zubairu Dada yace alakar da ke tsakanin kasashen ta karu sosai musamman bayan zaman da aka yi a 2021.
Matsalar tsaro a Najeriya Da sanyin asubar Juma’a aka ji labari miyagun ‘yan bindiga sun aukawa wani kauye da ke karkashin garin Zurmi a Zamfara, sun dauke Mai garin da kaninsa.
‘Yan bindiga sun yi hakan ne domin nuna fushinsu saboda an karbe masu babura. Mun ji labari cewa sun bukaci a biya fansar N5m, kuma a dawo da baburan.
Source:legithausang