Miyagun ‘yan ta’adda dauke da bindigogi sun kai farmaki masallaci a garin Maigamji dake karamar hukumar Funtua ta jihar Katsina.
An gano cewa sun bindige Liman inda suka tasa keyar mutanen da har yanzu ba a san yawansu ba yayin da wasu suka arce.
Lamarin ya faru a daren Asabar, 3 ga watan Disamba wurin karfe 7:40 yayin da jama’a suka taru suna sallar Isha’i a Masallacin.
‘Yan ta’addan dake cin karensu babu babbaka a dajin Funtua dake karamar hukumar Funtua ta jihar Katsina a daren Asabar sun kai farmaki wani masallaci inda suka kwashe masu bauta wadanda har yanzu ba a san yawansu ba.
Wani ganau ya bayyana cewa inda lamarin ya faru sunansa Maigamji dake karamar hukumar Funtua ta jihar Katsina, AIT ta rahoto.
Legit.ng Hausa ta gano cewa, garin Maigamji yana kan babbar hanyar Funtua zuwa karamar hukumar Dandume duk a jihar Katsina.
A kan wannan babbar hanyar ne zata sada mai tafiya zuwa har karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.
An kai farmakin Ana tsaka da sallah Kamar yadda ganau din ya sanar, an kai farmakin wurin karfe 7:40 na yamma yayin da Musulmi ke sallar Isha’i.
Yace ‘yan ta’addan sun tsinkayi Masallacin inda sama da masu bauta 50 suke sallah sannan suka fara harbi babu kakkautawa kafin su yi awon gaba da mutane da ba a san yawansu ba.
An tattaro cewa, sakamakon harbi, wasu jama’a sun samu raunika yayin da suke kokarin tserewa amma an gaggauta mika su asibiti.
Duk da ‘yan sanda ko wasu hukumomin tsaro dake jihar basu riga da sun tabbatar da faruwar lamarin ba, harin na zuwa ne bayan kwanaki kalilan da jam’iyyar APC mai mulki ta kaddamar da kamfen din ta na 2023 na jihar a karamar hukumar Faskari dake da makwabtaka da Funtua.
Makama a wallafarsu, sun sanar da cewa an halaka babban limamin Masallacin kuma Legit.ng Hausa ta tabbatar da hakan.
Kamar yadda Legit.ng Hausa ta bincika kuma aka tabbatar mata, har yanzu ba a tabbatar da yawan wadanda lamarin ya ritsa dasu ba.
An kuma sallaci gawar Liman kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
Malam Sa’adu Faskari, wani matashi mazaunin garin Maigamji inda lamarin ya faru, ya sanar da cewa makwabcinsa yana daga cikin wadanda lamarin ya ritsa dasu amma cikin karewar Ubangiji ba a tafi da shi.
Sai dai ya samu raunika a kafafunsa har da guiwar hannu duk wurin kokarin tserewa.
“Al’amarin akwai matukar firgitarwa. Allah bai yi da ni lamarin zai faru ba don a Masallacin nake sallah.
Sai dai nayi balaguro ne zuwa garin Dandume wanda kuma nayi dare sai na yanke hukuncin kwana a can.
“Mummunan labarin ya riske ni inda na dawo da safe na samu jana’izar Liman.”