Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta damke wani gagararren fitaccen dilan wiwi mai suna Ukashatu Idris ‘Dan asalin kauyen Kiyaki a Bungudu.
Matashin mai shekaru 25 a duniya an kama shi da buhu 27 na ganyen tare da sinki 31 na kwayar Exol da sunki 30 na Tramadol.
Ya bayyana cewa yana siyo buhu daya kan N30,000 amma ya siyar a N60,000, lamarin da yasa ya bar sana’ar gasa kajin da yake yi a baya.
A kalla buhuna 27 na busasshen ganye da aka boye cikin garri wanda ake zargin tabar wiwi cewa tare da sunki 31 na kwayar Exol tare da sunki 30 na Tramadol ‘yan sandan jihar Katsina suka kama.
A wurin kamen, an damke gagararren matashi da ya shahara wurin dillancin wiwi mai suna Ukashatu Idris na kauyen Kiyaki a karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah a wata tattaunawa da yayi ga manema labarai a hedkwatar rundunar dake Katsina, yace an kama Idris a ranar Talata, 25 ga watan Oktoba bayan samun bayanan sirri.
Ya kara da cewa, dubun wanda ake zargin ya cika bayan ya bi tititin Funtua zuwa Gusau dauke da buhuna 27 na ganyayyaki busassu wadanda ake zargin wiwi ce.
Kakakin rundunar ‘yan sandan yace a yayin bincike, wanda ake zargin ya amsa laifinsa na cewa ya kwaso ganyayyakin ne daga Auchi a jihar Edo zuwa Zamfara.
Wanda ake zargin ya kara da bayyana wani Kabiru Master dake yankin Lalan a Gusau wanda yanzu ake nema a matsayin abokin aika-aikarsa.
“Wannan ne karo na uku da nake wannan kasuwancin.”
Wani Nasiru ne ya nuna min harkar, a baya ina gasa kaji ne da soya kwai a yankinmu kafin in samu wannan kasuwancin mai ci wanda yanzu aka kama ni a Unguwar Dahiru ina yi.
“Kowanne daga ciki buhunan nan muna iya siyar da shi kan N60,000. Muna siyansa kan N30,000.”
– Wanda ake zargin yace, NDLEA Ta Bankado Babban Dakin Ajiye Hodar Iblis, Ta Kwace Mai Darajar Biliyan N193bn
A wani labari na daban, jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, sun farmaki wani babban dakin ajiya a yankin Ikorodu da ke jihar Lagas inda aka kama hodar iblis da ya kai nauyin tan 1.8 (kilo 1,855).
Darajar wannan hodar iblis da aka kama a dakin ajiyar ya kai $278, 250,000 wanda yayi daidai da biliyan N194, 775,000,000, jaridar PM News ta rahoto.
Source:legithausang