Kimanin kaso 6 na mutane a fadin duniya ne suka yi ammana cewa, nan gaba, duniya za ta kasance karkashin iko kasa daya tilo wato ko Amurka ko kasar Sin, yayin da kaso 34, rukuni mafi yawa, suke ganin cewa, abu mafi yuwuwa shi ne, samun kasa fiye da daya mai karfin fada aji a duniya fiye.
Wannan sakamakon nazari ne da cibiyar bincike ta CGTN da cibiyar tattara ra’ayoyin jama’a ta jami’ar Renmin ta kasar Sin suka gudanar, wanda ya nazarci wani kaso na mutane daga kasashe 22, ciki har da Amurka da New Zealand da Japan da Indiya da Masar da Nijeriya.
A wani labarin na daban dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana matsalar karancin man fetur da kuma shirin sauya fasalin kudi da Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya bullo da shi a matsayin wani shiri na kawo tsaiko ga zabe mai zuwa.
Tinubu ya bukaci ‘yan Nijeriya da kada su bari karancin man fetur ya sanyaya musu guiwa kan gudanar da ayyukansu na yau da kullum.
Tinubu ya bayyana karara cewa karancin man fetur da ake fama da shi tamkar zagon kasa ne sannan ya danganta lamarin da cewar da gangan na haddasa shi.
Dan takarar na APC ya bayyana haka ne a Abeokuta, yayin yakin neman zabensa a Jihar Ogun.
Yayin zargin cewar an hada baki da yin barna wajen samar da wutar lantarki, inda ya danganta sauya fasalin kudade da aka yi a matsayin wani shiri na dagula wa mutane lissafi.
“Ko sun ce babu mai a kasa, za mu yi tattaki don kada kuri’a. Sum yi barna da yawa don haka za su iya cewa, babu mai. Wannan zai iya haifar da rikici ta hanyar zagon kasa ga wadatar mai a kasa.
“Suna yin zagon kasa ga samar da mai. Ko man fetur ko babu za mu je mu kada kuri’a kuma za mu yi nasara. Wannan juyin juya hali ne mafi girma kuma idan na fada muku, kun san abin da nake nufi. Kun san ni ne zan sauya komai.
“Sun yi ta shirin haifar da matsalar mai, amma a manta da komai. Ni, Asiwaju zan magance matsalar samar da mai har abada.
“Ni dan gida ne, na zo nan, kuma ba zan ba ku kunya ba, za mu karbi mulki.
“Wannan juyin juya hali ne, wannan zabe juyin juya hali ne. Sun yin makirci, amma za su sha kasa. Sun ce farashin mai zai karu kuma zai kai Naira 200 kowace lita.Ba sa son a gudanar da wannan zabe, suna son a murde shi,” in ji Tinubu.
Da yake magana game da tsare-tsarensa ga matasan Nijeriya, Tinubu ya yi alkawarin bullo da shirin ba da lamuni ga dalibai, tare da samar da tsarin ilimi wanda zai magance matsalolin malamai da tabbatar da cewa dalibai sun kammala karatu a lokacin da ya dace.
“Ina ba ku tabbacin abu daya: zan bai wa dalibai lamuni. Babu wanda zai daina zuwa Jami’ar saboda kudin makaranta. Ina ba ku tabbacin cewa babu wanda zai sake maimaita shekaru ba tare da ya kammala karatunsa ba.”